Yadda ake kunun aya
Yadda ake kunun aya
Abubuwan bukata
1. Aya
2. Kwakwa
3. Dabino
4. Coconut flavour
5. Madara ta gari ko ta ruwa.
6. Sikari kadan.
Da farko zaa samu aya a jika ta domin a cire mata datti da kuma kasa da duwatsu dake cikin ta bayan an cire mata datti sai a ajiyeta a gefe sannan a dauko kwakwa a fasa ta a wanke wasu kanyi amfani da ruwan kwakwar a wurin hadin kunun ayar musamman idan masu zaki ne wasu kuma sukan zubar . Daga nan sai a aje kwakwar a gefe sannan a dauko dabino a bare shi daya bayan daya a saka ruwa a cire masa datti sannan a jiye already madara itama an tanada da kuma coconut flavour da kuma sikari domin bada dandano mai gamsarwa. Daga nan sai a hade duk wadannan abuwawan da aka gyara a guri daya sai a markada su sosai sai sunyi laushi sannan azo a samu rariya mai kyau wadda keda laushe sosai kamar irin na tankade gari sai a tace wannan hadin da aka markada a tabbatar b wani tuka na aya ko kwakwa da ya shiga. To daga nan shikenan kunun aya ya zama ready sai a zuba a cup a saka kankara ko asaka a fridge yyi sanyi domin kara fitar da dandanon shi ....Asha dadi lfy.
0 Response to "Yadda ake kunun aya"
Post a Comment