-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tallafin Noma: An Fara Shirin Tallafin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP) - Yadda zaku cike

Tallafin Noma: An Fara Shirin Tallafin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP) - Yadda zaku cike

Tallafin Noma: An Fara Shirin Tallafin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP) - Yadda zaku cike

Domin shiga cikin wannan shirin ga maza da mata, sai a danna wannan lambar: 347781.

Za a tambaye ku wasu bayanai kamar haka:


1. Cikakken Sunanka

2. Nambar Wayarka

3. NIN Number (Lambar Shaidar Zama Dan Kasa)

4. Jiharka

5. Karamar Hukumarka

6. Mazabarka

7. Kalar Sana’arka


 Muhimman Abubuwan da Ya Kamata a Lura:

- Ka cika dukkan bayanan da za a tambaya da cikakken bayani da kulawa.

- Lambar wayar da zaka yi amfani da ita wajen danna code ɗin *347*781# ta kasance ita ce ka yi rijistar NIN dinka, kuma ita ce ka yi rijistar BVN da asusun ajiyarka.

- Wannan tsari zai taimaka wajen saurin tantance bayanai, kuma zai saukaka wa gwamnati gudanar da tsare-tsaren tallafi cikin sauƙi.


 Wasu Muhimman Nasihu:

- Cika fom ɗin sau ɗaya kacal ya wadatar, sannan ka yi addu’a Allah ya bada sa'a.

- Idan kana da wasu mutane da suke bukatar tallafi, zaka iya cika musu fom dinka matuƙar suna da NIN Number koda ba su da asusun banki.

- Dangane da sana’a, a lokacin cike fom, zaka iya zaɓar sana’o’in kamar haka:


   - Noma

   - Kiwo

   - Dinki

   - Kwalliya (Cosmetics)

   - Kasuwanci

   - Saye da sayarwa

   - Kiwo na kaji ko dabbobi

   - Saloon

   - Wanzanci

   - Da sauransu.


- Ba lallai sai ka zabi wasu sana’o’i da suka fi karfi ko girma ba; ka duba na kusa da kai wanda kake da ilmi ko kwazo a ciki.

- Idan ka cika maka da kanka da matarka, ko budurwarka, ko yan uwanka da abokan arziki, ka tabbata suna da NIN Number, koda kuwa ba su da asusun banki.


 Shawara ga Mutanen Karkara:

- Idan kana da ‘yan uwa a karkara, ka basu wannan lambar su yi sauri su cike, domin za a dace in sha Allah.


Wannan shirin shi ne na farko a karkashin wannan gwamnatin, kuma an fitar da shi domin tallafawa mutane cikin tsarin gaskiya da adalci.


Lura: Bayan an cika fom din, za a ba da ID Number; ka adana wannan lambar saboda za a iya buƙatar ta nan gaba.


ALLAH Ya ba mu sa’a.

1 Response to "Tallafin Noma: An Fara Shirin Tallafin Kungiyar Matan Najeriya don Cigaban Noma (NWAP) - Yadda zaku cike"