zaman zawarci ayau - Matsalar 'ya Mace
zaman zawarci ayau - Matsalar 'ya Mace
Wannan shine qalubale da Mata ke fuskanta a yanzu.
Zaman zawarci zaman haquri ne bayada dadi.
Zawarci na nufin zaman bayan rabuw da miji, wata qila mijin ya rasu ne ko Kuma sabani ya kawo rabuwar aure
Y kamata macen da ta tsinci kanta a irin wannan yanayi tayi haquri , haquri sosai, saboda zata fuskanci abubuwa daga wurin iyaye, abokanai da Kuma mutanen ta na kusa.
Za'a tsangwameki musamman idan ba mutuwa ta rabaki da miji ba, za,'a na rinqa fadin kin kashe aurenki, kokin qi zaman aure, wanda masu fadar haka Basu ma taba yin aureba ko Basu San abinda ya rabaki da miji ba.
Wurin iyaye ma , sai Wani abu ya samu, sai ace inda kina gidan mijinki ai da kin huta. Yanayi zai iya zuwa da da gidanku Babu sararin da ma za'a ciyarda ke sai biyu ko sau uku a yini, idan kina zawarci sai a ga kin qara dawainiya musamman idan da yara kika zo, saboda haka ya kamata duka macenda take zawarci ta kama sana'a domin taimakawa kanta da Kuma na kusa da ita.
Y kamata iyaye su sawa Mata masu zawarci ido, da zarar sunga tana guntuwar mu'amala da namiji to idan tana son shi a gaggauta yin aure kana labari Kuma yasha ban ban.
Maganar gaskiya, mace mai zaman zawarci bisa ko wane lamari da zai zo Mata haquri shine abinda zatayi da yafi komai.
0 Response to "zaman zawarci ayau - Matsalar 'ya Mace"
Post a Comment