Zaman Budurci
Zaman Budurci
YANDA AKE ZAMAN BUDURCI
Zaman budurci zamane wanda mace take qarqashin iyayenta Kuma girma y kawo Mata.
Zamn budurci indai akwai iyaye a raye Kuma suna tsawata abin zaiyi dama, saboda lokaci ne da ya kamata ana lura da duk Wani motsi na yarinya , saboda a lokacin take Jan hankalin mutane sosai musamman maza.
A lokacin budurci mace y kamata ta kula da irin qawayen da zatana mu'amala dasu, saboda a wannan lokacin shi ne dai dai lokacin da abokanai da halayensu suke tasiri ga mutum.
Y kamata mace ta kula da kanta, ta riqe mutuncinta, tasan cewa tanada kina, ba kowane abu y dace tayi ba saboda takai munzali.
Mace da take lokacin budurci y kamata ta zama mai tsabta, saboda yanayinta ya canja, Yana buqatar kula ta musamman, uwaye musamman mahifiya y kamata ta taimakama erta sosai wurin hakan.
Mace da take cikin lokacin budurci y kamata ta rage ko ta daina mu'amala ta kusa da namiji saboda gudun faruwar barna.
Abuna qarshe yayin da mace take cikin lokacin budurci y kamata ta alaqnta duk Wani namiji da yyi Mata mgnar aure da iyayenta saboda Wani manufa ta daban yakeda.
Iyaye su dage d yiwa yaransu addu'a, Suma yaran su dage da addu'a domin neman kariya.
0 Response to "Zaman Budurci"
Post a Comment