-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Zaman Aure Ayau - Rayuwar Ma'aurata

Zaman Aure Ayau - Rayuwar Ma'aurata

Zaman Aure Ayau



Zaman aure zamane na har abada, dukkanin ma'aurata y kamata su sa aransu cewa ibadah suke yi, Kuma zamane zasuyi har na qarshen rayuwa idan hakan a rubuce yake.  Ita rayuwa da anyi aure ko haqiqa an shiga Wani sabon babi na rayuwa mai cike da qalubale , zamane wanda an riga an hadu waje daya komai wuri daya akeyi, don haka sai haquri. Zaman aure zamane na soyayya, jindadi, farin ciki, qaruwa da Kuma haquri. Idan akayi aure akwai soyayya da ma'aurata suke nunawa junansu mussan kafin zama yyi nisa. Aure zamane na jindadi da Kuma kwanciyar hankali, ana samun nutsuwa idan aure muddin akwai haquri d Kuma qauna. Zaman aure zamane na qaruwa( haihuwa). Kowase ma'aurata suna son  qaruwa a tsakaninsu, wanda addini da al'ada duka suna son hakan.

Idan aka fara samun qaruwa a aure so da yawa shine ta inda aure ke fara samun sabani idan ba haquri. A wurin mace, kyawon zaman aurenta tayi biyayya ga mijinta muddin abinda y buqata bai saba wa shari'a ba Kuma bazai cutarda ita ba. Yanayin zamnatakewa cikin gida, idan kin fita waje duka y kamata mace ta kiyaye abinda mijinta yakeso da wanda bayaso saboda ta kiyaye. Y kamata mace ta karanci mijinta tsaf, ta yanda zata yimasa Abu tun kafin y furta ko ya nema.   Mace idan tayi aure y kamata ta kama kanta, ta banbanta kanta da Mata wadanda basuda aure, ta rinqa karrama aurenta. Yana daga cikin abubuwan da y kamata mace tayi bayan aure, kula da kanta, kula da mijinta, kula d gidanta, tsabta, kwalliya da Kuma Mafi muhinmanci sanin sitting girki da Kuma mu'amala ta auratayya. Y kamata mace ta iya kwantarwa mijinta da hankalinsa a kowane lamari, tayi bashi magana mai dadi ta yanda zaiji dadi.  Y kamata mace ta kasance mai haquri da juriya a gidanta, tayi haquri amma bawai haqurinda zai cuta Mata ba. Tsakanin mace da namiji ya kamata kowa yayi haquri da Wani saboda yanaayi na zamnatakewa. Bahaushe yace zo mu zauna, zo mu Saba. Idan babu haquri zaman aure baya Kai ko Ina. Sannan matsayinki na mace idan miji yace kinyi laifi to ki Saba da bada haquri, ba abinda hakan zai rage ki dashi face zakiyi fari ne a wurin mijinki, saboda haka fada da hayaniya ba naki bane. Ki kula da dukiyar mijinki da Kuma son duk abinda yake faranta mashi. Namiji Kuma, y kamata ya sauke nauyin da Allah y dora masa na ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, iliminta da Kuma lafiyarta.

Y kamata namiji ya rinqa kyautatawa matarsaya Kuma iya yaba mata a duk abinda tayi musamman kwalliya da girki. Namiji kar ya zama mai nauyin hannu a gidansa, hakan ba kyau, sannan duk soyayyarda mace take maka idan ta gane baka son fitarda kudi ayi lalura to labari zaisha ban-ban. Namiji ma ya kamata ya iya haquri da matarsa saboda Mata rauni ne dasu, idan tayi abin fada, sai ayi fada na fahimta bana tashin hankali ba .Sannan abu Mafi daraja ya kamata ma'aurata su riqe sirrinsu dana gidansu, banda fallasa juna a wurin qawaye koma wani gurin daban. Abu na qarshe Banda yawan Kai qara wajen iyaye ko en uwa, hakan yana haifarda fitina a zaman aure, saboda tsakanin mata da miji sai Allah, zaki iya manta abinda miji yyi miki ki yafe, amma idan kin gayawa iyaye ko en uwa har su mutu basu mantawa kuma zasu ringa ganin baqin mijinki a Koda yaushe. Ma'aurata su Saba da daidaito tsakaninsu.

0 Response to "Zaman Aure Ayau - Rayuwar Ma'aurata"

Post a Comment