YANDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE
YANDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE
Shi rashin sani yafi dare duhu, Kuma duk abinda mutum bai koya ba zaita bashi wahala ne,
Mallakar miji hanyoyi ne daban daban, wadanda addini y koyar d Kuma wadanda muke koya al-adance.
Abu Mafi Muhinmanci wurin mallakar miji shine Addu'a, a duk lamari na rayuwa addu'a itace ginshiqi, wasu abubuwan ko ka yisu dole sai ka nemi taimakon ubangiji domin samun dacewa.
Abu na biyu shine ladabi d biyayya g miji. Ba ta yanda za'ayi namijin d akewa biyayya ana biyamasa dukkanin buqatunsa gwargwadon iko ace Kuma sai an hada da bin bokaye ko wasu malamai d suka Saba ma shari'a.
Al-ada d addini duk sun fadi biyayya a matsayin Wani bangare da kesa mallakar zuciyar namiji muddin abinda yakeso bazai cutarda ke ba ko Saba ma shari"a.
Abu na uku shine iya girki. Girki Wani abu ne na musamman Dake janyo hankalin da namiji zuwaga 'ya mace. Girkin Kuma y kama daga dafashi, yanda zaki sakashi d Kuma yanda zaki bayarda shi. Sannan zama kusa d miji yayin da yake cin abinci ana taimaka mashi d wasu abubuwa, fira da sauransu akwai alfanu a hakan .
Yanayin tarbo na miji idan y shigo gida.
Wannan wurin hausawa an barmu a baya, ba mada qoqari tarbar miji idan y shigo gda, basai na tafi d zurfi ba, ko wace mace tasan abinda mijinta yakeso a tarbeshi da shi idan y shigo gda, wata ko Kalmar sannu d zuwa miji baya samu wurinta balle wasu abubuwa na nuna soyayya, wanda hkan na rage soyayya tsakanin ma'aurata
Tsabta.
Tsabta a kowane nau'i na rayuwa tanada matuqar tasiri, haka ma ko a fan in mallakar miji tanada fa'ida, kama daga tsabtar muhalli, jiki, kayan miji, kayan yara d Kuma qamshi. Mace ai er qamshi aka Santa.
Kwalliya.
Iya Ado, sa sutura, yanayin tafiya, kitso, lalle yana janyo hankalin miji.
Abinda wata mijinta yakeso wata nata mijin bayaso, y kamata ko wace Mata ta karanci halin mijinta na sanin abinda yafi so d wanda bayaso.
Iya zance/magana/lafazi
Magana mai dadi ma ai sadaqa ce inji fiyayyen halittu, balle tsakanin Mata da miji idan qauna take d tausayi d soyayya.
Iya magana na karkato hankalin miji zuwa ga mata, yanayin maganar, sautin maganar d Kuma yanda ido suke nunawa lokacin maganar.
Koda bata wa miji rai akayi, inma cikin gda inma waje, idan kin iya mgna mai dadi, take zaki kwantarwa mai gda da hankalinsa.
Sai qarshe iya mu'amala ta auratayya tana cikin manyan sirrikan mallakar miji cikin sauqi.
Mata mu tashi tsaye mu kama mazajenmu, muyi ma kanmu wa'azi kan abinda y dace, zuwa wurin bokaye ba namu bane.
Idan bokaye nada maganin buqatunmu, su yima kansu mana, wadanda ko suturar kwarai ta gagaresu sai kudadenmu d suke karbewa suns samun na abinci mu Kuma su barmu da fushin ubangiji.
Allah y datadda mu.
0 Response to "YANDA ZAKI MALLAKE MIJINKI A SAUKAKE"
Post a Comment