-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YANDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI

YANDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI

YANDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI

Zama da talakan miji ba Wani abin fadi bane ko tashin hankali, idan akwai soyayya, qauna d tausayi junab wata damuwa aciki. Sannan Kuma talakan d mai kudin duka Allah ke yinsu Kuma shi yake basu, idan d rayuwa watarana Baku rabo zai zo.

Talauci baya tabbata har abada haka ma arziki baya tabbata har abada .

Talakan miji y kasu kashi daban daban g nawa tunani.

Akwai talakan da bayada ko sisi Kuma baya iya wadatadda iyalansa d abinci d buqatu na yau d kullum.

Akwai talakan da bayada kudi amma Kuma kullun da dubara sai iyalansa sun samu abinda sukayi.

Akwai talakan da yanada en canjinshi amma sai dai yyi hidimar gda amma ba'a samun abubuwan more rayuwa .

Ita Kuma macen da zata zauna d talakan Suma iri biyu ne zuwa uku.

Akwai macen da take sana'a.

Akwai macen d bata sana'a.

Akwai macen da gidansu akwai rufin asiri 

Macen da keda sana'a zata iya zama da kowane daga cikin wadancan kashin mazajen talakawa , zata iya anfani d 'yara ribarta ta biya musu buqata na abinda bai gagara ba , inma su kadai ko Kuma d yara indai d fahimta tsakaninsu , shi kuma namiji yaji tsoron Allah wasu idan suka ga mata na taimaka musu sai su barsu d lalurar gdan, ranarda ma suka samu abin anfani basa shigowa dashi gida balle a anfana, ta hakan wata bata gane mijin y samu ko bai samu ba, saboda mugun hali, amma idan d fahimta baza'a samu wannan ba.

Macen da bata sana'a, ita kam akwai damuwa, saboda sai dai haquri don watarana sai an wayi gari ba'a ciba, saboda miji babu ita ma babu, tau sai dai haquri d abinda y samu.

Macen da gidansu suke da rufin asiri zata iya nema masu abinda zasu ci indai ba matsala daga wurin uwayenta, don su samu su rufa ma kansu asiri.

Yanada muhinmanci ki iya godiya ga mijinki a komai qanqantar abinda y samo, hakan yana sa yaji sanyi a ranshi ya ga an yaba abinda ya kawo.

Sannan mace ta rinqa ma mijinta addu'a da fatan alkhairi a duk abinda yyi ko ya bata, ko ya bayar ko bai bayar ba.

Watarana mijin sai shigo rai bace saboda Babu, kiyi qoqari kwantar masa d hankali, ki nuna mai babu komi, yau da gobe sai Allah, watarana duk yanayinda kuke ciki zai zama labari.

Sannan ko tambayar miji Abu zakiyi kar like gatsau Ina son Abu kaza, a'a, maigida don Allah idan akwai sarari inason Abu kaza, zai ji dadi Kuma ko bayada a wannan lokacin idan y samu sai y baki.

Kuma a ko yaushe kar ki Rena kanki don kina zama da talakan miji, ki godewa Allah, shi zai kawo maku fita.

Mata kar ku addabi mazaje d masifa akan babu, ga babu, ga masifa, rana zafi inuwa quna kenan, sai miji ya fita hayyacinshi ko ya fara wasu mugayen dabi'u musamman shaye-shaye saboda bayada walwala.

Wasu halaye Mata su suke saka mazajensu aciki.

Da qarshe mata ku kama sana'a ko ya take indai ana samun Wani abu, sana'a tafi maula da roqo.

Kar ku rena sana'a, bahaushe ma yace marena kadan barawo.

Maza Kuma ku kama sana'a musamman sana'ar hannu, saboda a duk rintsi sana'ar hannu baiwa ce d babu wanda zai iya kwace maka.

0 Response to "YANDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI"

Post a Comment