YANDA AKE ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI
YANDA AKE ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI
Duka namijin da yake zama da mace ma'aikaciyar gwamnati yana da qoqari da Kuma haquri gsky.
Ba kowane namiji yake iya bari mace tayi aiki ba musamman aikin gwamnati da aqalla ana fita kusan kwana biyar a sati, Kuma kullun sai anje.
Duk macen da take aiki y kamata tayi taka tsan tsan da yanayin aikinta da Kuma karrama da darajta aurenta.
Namiji mai auren ma'aikaciyar gwamnati sai y taimaka da Kuma tashi tsaye wurin bata shawarwari gameda lamarin aikinta da Kuma aikin gidanta.
Kada namiji y walaqanta kanshi saboda matarsa na samun Wani abu qarshen wata, ya tashi tsaye da gidanshi, y nuna shi namiji ne, yayi Mata duk dawainiya da miji y dace yawa matarsa gwargwadon yanda zai iya.
Namiji y kama yaransa, ya sadu a jiki, ya Kuma kyautata haqqinsa na zama Uba a garesu kada y bari matarsa saboda yanayin aiki tayi wasa da tarbiyyar yaransa, Kuma kada y yadda ace ita take kula d dawainiyar yara, ta hakan Wani abu makamancin raini da walaqanci zai shiga.
Mace Kuma saboda kina aiki bashi zaisa kiga kamar kina cin gashin kanki bane, ki tuna ko yaushe cewa je a qarqashin Wani kike.
Sannan duk macen kirki ma'aikaciya y kamata tasa hannunta wajen lalurorin gida inda ya dace, ta taimaka ma mijinta basai y roqa ba, wasu qanunun abubuwa basai kin tambaya ba zaki iya yima kanki da yaranki.
Ya kamata mijinki y Mori abinda kike samu indai kinda tunani, Kuma ai inda kin lura duk abinda kikayi qaruwar kuce ke da shi.
Ki tsare mutuncin aurenki, saboda za'a na cudanya da maza da Kuma mutane daban daban.
Ki zama mace wacce tasan kanta.
Sannan saboda kina aiki kar ki rena mijinki, ki girmamashi, ki mutuntashi, sannan banda gori, banda gori, banda gori, saboda ko fiyayyen halitta ma y fada wannan yana cikin hali na mata.
Abu na qarshe ga nawa tunani banda ajiye er aiki a gida wai tayi miki abinci ta kula da yaranki, wannan kwata-kwata ba tsarin matan da suka San kansu bane.
Madallah da namijin da yake zaune da ma'aikaciyar gwamnati.
Haqiqa shi jajirtacce ne.
0 Response to "YANDA AKE ZAMA DA MATA MA'AIKACIYAR GWAMNATI"
Post a Comment