-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Auren Mini Ma'aikacin Gwamnati - Zaman Aure

Auren Mini Ma'aikacin Gwamnati - Zaman Aure

Auren Mini Ma'aikacin Gwamnati - Zaman Aure

YANDA AKE ZAMA DA MIJI MA'AIKCIN GWAMNATI

Miji ma'aikacin gwamnati mutun ne wanda yake fita aqalla sau biyar a sati, sannan Mafi yawancin lokutan tashin shi bayan la'asar ne, wasu Kuma bayan azahar.

Macen da take zaune da miji ma'aikacin gwamnati ya kamata ta kiyaye wasu abubuwa.

Na farko, ya kamata mace ta kiyaye lokacin fitar mijinta da dawowarsa domin shirya masa. Sannan y kamata tasan hakan ko don watarana idan y wuce lokaci Kya iya bincika ko lfy.

Sannan abu na biyu, Yana da kyau mace ta rinqa Kiran mijinta idan y fita a qalla sau daya ko sau biyu kafin ya dawo gida saboda raya soyayya, sannan Kuma Kuma iya yin hkan Yana samuwa ne idan yanayin aikin mutun ya barshi.

Mata su kiyaye da Wani abu, ba sai kina buqatar Wani abu a wurin mijinki zaki kirashi ba, hakan ba dai dai bane, Kuma Yana kawo sabanin fahimta.

Sannan mace tasan da mijinta ma'aikacin gwamnati indai ba Wani aiki yakeyi gehe ba,   to samunshi Qarshen wata me, y dogara ga albashi, saboda haka, kisan yanda zaki nemi abu a wurinshi, d Kuma lokacin da ya kamata ki nema.

 Sannan Mata su rinqa kyautatawa mazajensu zato, game da mu'amala ta wuri aiki. Tabbas, yanayin ynzu aikin gwamnati, Mata da maza ne ke gudanar dashi, kada mace ta Kira mijinki don harka ta wurin aiki ki kama tada jijiyoyin wuya, hakan da na sani kawai yake haifarwa.

Namiji Kuma y kamata y kiyaye yanayin mu'amalarsa da Mata wajen aiki, ya riqe mutuncin aurenshi ta yanda za'a gujewa tashin hankali.

0 Response to "Auren Mini Ma'aikacin Gwamnati - Zaman Aure"

Post a Comment