-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Auren Attajirin Miji

Auren Attajirin Miji

Auren Attajirin Miji



YANDA AKE ZAMA DA ATTAJIRIN MIJI.

Zama da attajirin miji kusan banbancinsa da zama da sauran mazaje bayada Wani yawa sosai.

Har wayau zama d kowane kalar miji, soyayya, qauna da tausayi sune jigo, muddin akwai wadannan zaman zaiyi dadi.

Shi attajirin miji ana nifin mai tarin dukiya kenan .

Abu na farko idan mace na tare da attajirin miji ya kamata ta rinqa taimaka mashi wajen tunatarda shi abubuwan da zasu sa y tsira ta sanadin dukiyarsa ba wai a jefa shi a mahallaka ba.

Nuna miji taimakon 'yen uwansa shine Abu Mafi kyau, saboda bayada abin da yafi mishi su a duniyar nan, y kamata idan yana cikin walwala su sani, Kuma su gane. Kyautatawa en uwa ma a addinance but ne mai matuqar kyau Kuma ga tarin lada.

Idan mahaifiyarshi na raye a nuna mashi hanyoyinda zai taimaketa, yyi Mata duk abinda ta buqata gwargwadon iko, idan yana kyautatawa en uwansa mahaifiyar zatayi matuqar farinci, haka zalika idan bata raye sune yake gani yaji cewa shi Yana da wasu d zasu iya zama madadin mahaifiyarsa a wurinsa.

 Sannan ke a matsayin matar idan en uwansa suka ziyarce ku duk Wani abin alkhairi da bai gagara ba sai kiyi musu zasuji ddi Kuma mijin ma zayaji dadi, ta haka shi zai iya taimakon en  uwanki ko mahaifiyarki b tareda ke nemi hakan ba.


Na biyu Lularda shi akan taimakon maqwabta da Kuma abokanai na kusa.

Addinance makwabaci yafi kowa zama kusa dakai, y kamata idan kana cikin walwala ya sani, idan kana cikin yanayi na qunci ya sani.


Na uku taimakawa mijin wajen tunatarda shi da kama mashi yin sadaka, dukiyarsa zata anfaneshi ne ta wannan hanyar, abinda mutum yyi sadaka dashi shine nashi, idan baya gida a tunatardashi yyi, sannan Mata zata iyayi a maimakon mijinta, shi ya samu lada itama ta samu.


Na hudu tattali. 

Saboda kina zaune da attajirin miji bashi zaisa ki rinqa yanda kika ga dama d dukiyarsa ba, Banda almubazzaranci, shi din haramun ne, a taimaka a bama mabuqata, Kuma ayi komai iya yanda ya kamata .


Na biyar kula da yaransa ta hanyar basu tarbiyyar rashin walaqanta mutane saboda mahaifinsu na da dukiya, hakan ba dai dai bane.

 Sanna Abu na qarshe yi masa addu'ar Allah y tsare masa dukiyarsa yasa ta anfaneku duniya da lahira .

Sannan Mata Muji tsoron Allah, da yawan masu auren maza masu dukiya su suke izasu ga mahallaka , mu tuna muma Muna da 'ya'ya, Kuma watarana Muna kyautata musu zaton rabo mai yawa d albarka, bama burin ayi mana abinda bai dace ba.

Allah ya sa mu dace.

0 Response to "Auren Attajirin Miji"

Post a Comment