Ana ci Gaba da Cike Aiki a Ma'aikatar Man Fetur ta Najeriya (NNPC) Limited
Ana ci Gaba da Cike Aiki a Ma'aikatar Man Fetur ta Najeriya (NNPC) Limited
Yan Arewa Mu Farka: An Bude Shafin Daukar Sabin Ma'aikata a Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC)
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) Limited, kamfani ne mallakin gwamnati a Najeriya. A da, cikakken kamfani ne na gwamnati, an mayar da shi kamfani mai iyakacin alhaki (Limited liability company) a watan Yuli na shekarar 2022. NNPC Limited na da lasisi da za ta yi aiki a masana'antar man fetur ta ƙasar. Yana da haɗin gwiwa da kamfanonin mai na ƙetare don haɓaka albarkatun mai na Najeriya. A yanzu haka, kamfanin ya bude shafin daukar sabbin ma'aikata a sassa daban-daban cikin masana'antar.
Ranar rufewa cike aikin shine 20 ga Agusta, 2024.
Masu dole ne su cika waɗannan sharuɗɗan:
1. Mallaki takardar digiri na farko a Aji Na Farko ko Aji Na Biyu Sama.
2. Mallaki HND (Distinction).
3. Masu digiri na farko a Aji Na Biyu Kasa su mallaki digiri na Masters.
4. Masu HND Upper Credit su mallaki digiri na Masters.
5. Su kammala karatu daga jami'a/polytechnic/monotechnic mai izini ba kafin shekarar 2019 ba.
6. Su kammala NYSC.
7. Ba su wuce shekaru 28 zuwa 31 ga Disamba 2024.
8. Mallaki kyawawan kwarewar sadarwa, kwamfuta da kuma zamantakewa.
Yadda Zaku Cike
Masu sha'awar cikewa su latsa shafin yanar gizo dake a kasa domin cikewa:
Shafin Cikewa: [NNPC Recruitment]
Karin bayani: [NNPC Careers Eligibility]
0 Response to "Ana ci Gaba da Cike Aiki a Ma'aikatar Man Fetur ta Najeriya (NNPC) Limited"
Post a Comment