-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Abubuwanda ya dace kiyi lokacin da kike dauke da juna biyu

Abubuwanda ya dace kiyi lokacin da kike dauke da juna biyu

Abubuwanda ya dace kiyi lokacin da kike dauke da juna biyu

Lokacinda mace take dauke da juna biyu ya kama ta gane cewa ba ita kadai bace, tana dauke da jinjirin mutum a cikinta Kuma da yardar Allah wanda yake motsi( rayayye), saboda haka akwai abubuwanda ya kamata ta kiyaye.


Abu na farko, ya kamata mace mai juna biyu ta kula da lafiyarta, kada tayi wasa da hakan ko kadan, da zarar taji batada lafiya to taje asibiti a duba ta.

Wani ciwon Kai, ciwon ciki, kumburi da duk Wani abu da taji ya mata ba dai dai ba ko Kuma bata Saba ganinsa ba to tayi qoqari taje a binciki lafiyarta.

Haka zalika zuwa wajen awo asibiti na da matuqar anfani, hakan zai qara sa tasan yanayin lafiyarta da na abinda ke cikin cikinta .

 

Abu na biyu shine cin abinci ingantacce, wanda idan kika ciki zaki ji dadi, Kuma zaki natsu, sannan zai yimiki anfani da keda abinda ke cikinki.

A rage ko a guji cin abinci mai yaji, ko mai maiqo sosai.

Sannan a guji zama da wunya, saboda daga lokacinda mace taji tana Jin yunwa to lallai abinda ke cikinta shina buqace yake da abinci, ta abinda kika ci ne shima zai samu ya ci, don haka zama d yunwa na wahalarda jinjirin d ke ciki.

 Abu na uku shine, motsa jiki.

Duk wata mace mai ciki ya kamata ta rinqa motsa jiki wanda bazai wahalarda ita da abinda ke cikin cikinta ba, kada tayi zaune ba aikin komi daga ci sai kwanciya hakan na haifar da matsala yayin da kike dauke da juna biyu.

 Na hudu ki yawaita yin abubuwa na kwarai saboda tunanin abinda ke cikinta ya samu albarkar haka.

Sannan a yawaita addu'a saboda rabuwa lafiya da abinda ke ciki da Kuma nema masa albarka da tsari tun yana ciki har ya fito.

Sannan kisan yanayin kwanciyarki, akwai yanayin kwanciyar da yake haifar da matsala, misali kwanciya a jicce ko rai-ran, wannan ko addini ba yada kyau, haka zalika ko lokacinda mace take dauke da juna biyu ba ya haifar da da mai ido.

 Na qarshe Kuma shawarce Mata masu ciki ana Basu shawarar yawan cin dabino da zuwa, Yana gyara lafiyar yara da ke ciki .

0 Response to "Abubuwanda ya dace kiyi lokacin da kike dauke da juna biyu"

Post a Comment