Karin Bayani Akan Shirin "RENEWED HOPE CASH CONDITIONAL TRANSFER" Shirin Tallafin N25,000 na Gwamnatin Tarayya
Karin Bayani Akan Shirin "RENEWED HOPE CASH CONDITIONAL TRANSFER" Shirin Tallafin N25,000 na Gwamnatin Tarayya
Idan ka ga wannan sakon, gaskiya ne abinda ka gani, ba wasa ba. Sai dai ka dan jira zuwa lokaci kadan, za a kiraka ko a sake turo maka sako domin baka ATM din da zaka fitar da kudinka.
Shi wannan kudin na wadanda aka tura wa account daga Access Bank da Zenith a shekarun da watannin baya ne, amma a yanzu haka an kara da wasu bankunan da suka hada da Polaris da Wema Bank da sauransu.
Shirin na CCT PVHH HUG da sauransu shine wannan, shine wanda a baya aka dinga bawa mutane kudi a hannu wasu ta account suna cirewa. Shine wanda aka bawa mutane yellow kati 🟡 da blue🔵 da sauransu.
Shi ne wanda aka karbi bayanan mutane da iyalansu kusan sau uku a wasu daga cikin jihohin Najeriya.
Yana cikin wanda gwamnatin tarayya ta bada umarni kusan wata daya ko sama da haka aka dauki bayanan mutane.
Za a bada wannan kudi sau uku, in sha Allahu. Wadanda suka sami kudin RRR Direct kwanakin baya ba lallai suga irin wannan sako ba, domin su direct za suga kudinsu kamar yadda suka saba gani a baya tunda dama bayanansu yana cikin saba tun a farko.
Allah yasa mudace.
Jafar kawuwa
ReplyDelete