An Bude Shafin Cike Shirin ALAT na Bakin Wema na Kakar Hutun Zafi 2024 Wato "ALAT by Wema Summer Internship Program for Young Nigerians 2024"
An Bude Shafin Cike Shirin ALAT na Bakin Wema na Kakar Hutun Zafi 2024 Wato "ALAT by Wema Summer Internship Program for Young Nigerians 2024"
Shirin ALAT na Bakin Wema na Kakar Hutun Zafi shiri ne na makonni guda wanda Bankin Wema ya shirya domin karfafa matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 18 da kwarewa da ilimin da ake bukata don samun gogewa da bincike a fannin aiki tun daga matakin farko.
A lokacin shirin, mahalarta za su shiga cikin ayyuka daban-daban ciki har da tarurrukan karawa juna sani, ayyuka tare da juna, da gwaje-gwajen ainihi, kuma za su samu kwarewa da ilimi daga kwararrun masana da za su inganta kwarewarsu da basirarsu.
Shirin na shekara ta 2024 zai gudana daga ranar 1 ga Yuli zuwa 19 ga Yuli, 2024, a wasu rassa na Bankin Wema a fadin kasar.
Bangarorin shirin sun hada da:
1. Finance - Kudi
2. Legal - Shari'a
3. Human Resources - Albarkatun Dan Adam
4. Information Technology - Fasahar Sadarwa
5. Data Science - Kimiyyar Bayanai
6. Brands and Marketing - Alamu da Kasuwanci
7. Innovation - Kirkire-kirkire
8. Admin - Gudanarwa
Yadd zaku cike
Domin cike wannan shirin latsa shafin yanar gizo gizo dake a kasa
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSe_uAnMs5T2F1JmAS6hVlfW2yhAiFs40DsIuHUX5jGQlxC4PA/viewform
0 Response to "An Bude Shafin Cike Shirin ALAT na Bakin Wema na Kakar Hutun Zafi 2024 Wato "ALAT by Wema Summer Internship Program for Young Nigerians 2024""
Post a Comment