An Bude Shafin Cike Climate Smart Nigeria Tare da Hadin Gwiwar Glow Initiative for Economic Empowerment da Tallafi Daga Access Bank PLC (Ranar Rufewa: Yuli 24, 2024)
An Bude Shafin Cike Climate Smart Nigeria Tare da Hadin Gwiwar Glow Initiative for Economic Empowerment da Tallafi Daga Access Bank PLC (Ranar Rufewa: Yuli 24, 2024)
Sauyin yanayi yana lalata duniya. A Najeriya, tasirinsa ya haifar da matsanancin fari, hamada, ambaliyar ruwa, da rikice-rikicen tsarin saukar ruwan sama. Wadannan tasirin suna shafar lafiyar dan Adam, jin dadi da kuma muhalli. Amfanin gona ya lalace sosai wanda ya jawo talauci mai tsanani a arewacin kasar. Matsanancin ambaliyar ruwa da yaduwar cututtuka ta hanyar ruwa mai guba ana samun su a kudanci. Saboda haka ne Climate Smart Nigeria tare da hadin gwiwar Glow Initiative for Economic Empowerment da tallafi daga Access Bank PLC suke zuba jari wajen samar da sabuwar ƙarni na shugabannin makamashi matasa domin jagorantar canji wajen sauya makamashi da kuma daukar matakan sauyin yanayi a fadin Najeriya.
Shirin horarwa na shugabancin yanayi (Special edition for Energy Leaders) an tsara shi domin samar da horo na musamman ga wadanda suke cikin harkar ko kuma masu sha'awa da kuma niyyar yin canji a fannin girki mai tsafta, makamashi mai tsafta, hasken rana, da sarrafa shara zuwa makamashi kan fahimta da aikace-aikacen makamashi mai sabuntawa don ingantaccen yanayi.
Bayan horarwa, dukkan wadanda aka horar za su zabi makaranta daya inda za su koyar da sauyin yanayi da makamashi mai sabuntawa domin taimakawa wajen tarbiyantar da matasa masu kishin kasa wajen samar da al'umma mai jurewa sauyin yanayi. Dukkan wadanda aka horar za su samu kayan koyar da sauyin yanayi da kuma takardar shaida ta shugabancin yanayi.
Yadda Zaku Cike
Domin cike wannan damar latsa shafin yanar gizo-gizo dake a kasa
https://climateleadershipfellowship.org/climate-leadership-fellowship-application-form/
Allah yasa mu dace
Anas Yakubu
ReplyDelete