1000+ Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki da Jijiyoyin
1000+ Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki da Jijiyoyin
Kalaman soyayya masu dadi da ratsa zuciya suna da matukar muhimmanci wurin inganta soyayya tsakanin masoya. Ga wasu daga cikin kalaman da zasu burge masoyan ku:
Kalaman So Ga Budurwa
1. Masoyiya ta, kinsan meyasa nake kasancewa cikin farin ciki a koda yaushe? Ko wacce dare, muryar ki ke samar da natsuwa a zuciya ta kafin na kwanta bacci. Duk safiya inna tashi daga bacci, muryar ki ke samar mun da farin ciki. Da fatan kina lafiya.
2. Zai iya kasancewa, niba ajin ki bane, ba irin namijin da kike so bane, amma inaso ki saka a zuciyar ki cewa nayi alkawarin zama irin namijin da kike mafarkin samu a rayuwar ki, nidai dama nake bukata.
3. Ina so kiyi mun wata alfarma guda daya, inaso fuskar ki ayayin da kike murmushi ta zama fuskar da zan gani karshe kafin na kwanta, haka zalika fuskar da zangani bayan na tashi daga bacci duk safiya. Zaki iya bani wannan damar?
Kalaman So Ga Saurayi
1. Masoyi na, kasan meyasa nake son ka? Soboda babu abunda kafi so a zuciyar ka face sani farin ciki. Nazamo mace mai son namiji wanda zai damu dani, ya soni kamar yadda yake son kansa, kuma na sameka. Ina son ka.
2. Tunda nake a rayuwa ta, ban taba zaton zan shiga irin farin cikin nake ciki yanzu ba. Soboda kai, na daina shiga damuwa, na daina jin duk abunda mutane suke fada duk ta dalilin ka. Saurayi irin ka a wannan zamanin, kudi bai iya siyar su.
Kalaman Soyayya Text Message
1. Komai zai iya faruwa a wannan duniyar da muke ciki; zasu iya yuwa masu karfafa mana gwiwa ko kuma masu saka mana kasala, amma ina so kisan wani abu guda daya, duk halin da zan shiga ko zaki shiga bazai sa nadai na irin son da nake maki ba.
2. Idan aka tambaye ni menene nake tsoron rasawa a rayuwa ta sai nace soyayyar ki da yardar ki. Kina da matukar amfani a rayuwa ta kuma babu abunda wani ko wata zasuyi hakan ya sulwan ta.
Kalaman Yabon Budurwa
1. Masoyiya ta, samun ki a rayuwa ta kawai babban robone. Kafin haduwa ta dake, na kasance me kokwanto a kan zaki amince dani ko bazaki aminta dani ba, amma gashi cikin sauki nasame ki, gaskiya kina da kyakkyawar zuciya.
2. Bazan iya rayuwa babu ke a cikin ta ba. Kinriga kin sa na zama gwarzo, babu abunda nasa a zuciya ta sai kyatata maki. Dan nishadin da nake samu a wurin ki bazai misaltu ba. Ashirye nake namaki duk abinda zai saki farin ciki.
Kalaman Birge Saurayi
1. Ina son ka masoyi na. Duk abunda zaka fuskanta a wannan rayuwar ko alkhairi ko sharri ina mai tabbatar ma ina tare da kai. Nidai fatana mukasance tare a wannan duniyar masoya mai abun mamaki.
2. Har ila yau ina kara godewa ubagiji da ya hadani da saurayi wanda na dade ina mafarkin samu. Na dade ina rokar ubangiji da ya nuna mun irin wannan rana da zan sami saurayi wanda zai soni irin soyayyar da bazai iya misaltuwa ba kuma nasamu.
Kalaman Bada Hakuri a Soyayya
1. Masoyiya ta! Ina so na roki wata alfarma guda daya wurin ki, ina mai rokon ki kimanta da abunda ya faru a tsakanin mu, zuciya ta ta kasa hakura dake, nayi tinanin zan iya zama ba da tinanin ki ba amma hakan bazai yu ba. Zuciya ta tana kewar ki.
2. Haryanzu nakasa yarda cewa nina saka ki a wannan hali da kike ciki. Dan allah, kidawo gare ni masoyiya ta, munsamu sabani a tsakanin mu amma ba hakan zai zamo sanadiyar rabuwar mu ba.
Da wadannan kalaman soyayya, zaka iya inganta soyayyar ka/ki tare da masoyan ku cikin sauki.
0 Response to "1000+ Kalaman Soyayya Masu Ratsa Jiki da Jijiyoyin"
Post a Comment