-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA ZAKA ZAUNA DA MACE FIYE DA DAYA

YADDA ZAKA ZAUNA DA MACE FIYE DA DAYA

YADDA ZAKA ZAUNA DA MACE FIYE DA DAYA. 

Yakai mai gida amatsayinka na mai gida yayin da kake da mata sama da daya dole ne ka kwatanta adalci atsakaninsu,

DAIDAITO WAJEN TUFATARWA

yaVkansance kada ka baiwa wanan tufafi mai kyau mai tsada, ita kuma dayar daya ka bata Mara kyau ko me arha ko kuma kana yiwa mutane awaje iyalinka sedai taiwa kanta da yayanta, wanan zalunci ne kuma be kamata ba  riyace domin waje sunsan kana yiwa jama a amma iyalanka basu san kana yiba, ma ana baka wadatar dasu.

Idan yayi haka bada yaddar dayar ba to beyi adalci ba kuma idan ka kyautatawa na waje sama da iyalanka to kana tare da matsala babba awajen Allah se kayiwa Allah bayani saboda haka idan kanayi iyalanka su zasu fara bada shedar kirkinka, amma bawai iyalanka suna kuka suna nema ayi musu, kai kuma baka musu kana yiwa na waje domin neman suna to kusani cewa Allah ze saka mata.

DAIDAITO A KYAKYAWAR MU AMALA

ya kamata miji ya daidaita matansa wajen mu a mala kada ka yiwa dayar kyakyawar mu a mala dayar kuma kai mata mummunar mu a mala, Allah subhanahi wata ala yace kuyi musu kyakyawar mu a mala ga abinda aka Sani na al ada suratu nisa i (aya ta sha tara19 ) 

YIN HAKURI

Dukda cewa miji yana adalci dole nefa se yana hadawa da hakuri, hakuri anan  yana nufi, shi mijin se yanayin hakuri matukar shi aka yiwa laifin bai shafi hakkin Allah ba haka suma matan se Su rinka yi hakuri da junansu  alokacin da wani abu ya faru watarana za suga Alkhairin hakan, Ku sani cewa duk inda kuke sefa  kunyi hakuri koda kuwa agaban iyayen Ku kuke domin haka zaman tare ya gadar,

BOYE SIRRIN MATA

matsayinka na miji me mace fiye da daya kada namiji mai fiye da daya ya yadda ya zamo ace kai baka da aikin yi sai Bayyana sirrin wata ga wata ga iyalanka,

Duk mijin da yake yin haka ya tabbata cewa shine yake hautsuna gidansa da kansa ba wata ko wani ba, kuma irin wanan miji be kamata ya auri mace fiye da daya ba IYA SASANTA TSAKANIN JUNA 

Ana bukatar namiji mai fiye da mace daya ya dinga kokarin iya sasanta  tsakaninsu yayin da wani abu ya faru atsakaninsu, ya zamo mai adalci awajen sasanta tsakanin kada ka goyi  bayan wata saboda ita tafi kyautata maka kuma  ba a kan gaskiya take ba, idan wata ta cuci wata kai mata fada kai iya kokarin yi musu sulhu atasakanin su,

Wadannan sharudan sune ake so lallai mai aure mace fiye da daya ya cikasu kafin ya kara aure Idan bazaka iyaba to be kamata ka kara mace ba.

0 Response to "YADDA ZAKA ZAUNA DA MACE FIYE DA DAYA"

Post a Comment