YADDA AKE ZAMAN AURE A Yau
YADDA AKE ZAMAN AURE A Yau
Shawara ga ma aurata,
Kada kice zaki tada hankalinki da mijinki bashi da kudi koya talauci
Dukn talaucin mijinki kiyi hakuri ki zauna da abinki cikin kwanciyar hankali da soyaiya miji wata baifi mijinki ba duk sunansu mazajen aure kiyi alfahari da abinki ko a ina ne,
Naki shine naki mijin wata ba naki bane don haka ki tsaya ki nutsu ki rike mijinki cikin nutsuwar zuciyar da kulawa, ki dena hangen na wata ko abinda da ake mata,
Yadda ko wace zata fito tayi alfahari da abinta kima kiyi alfahari da naki, dake da matar governor da matar sarki duk sunanku matan aure watakil ma ki fisu samun kula da soyaiya don haka talaucinki ba aibu bane amma boyeshi shiyafi Alkhairi kinji,
Indai yana iya baki kokarinsa wajen kula dake to karki gaza kema, idan kin barshi ma baki san dawa Allah ze kara hada kiba kiyi hakuri ki zauna da abinki ,
Dayawa matan da kuke gani kuke sha a warsu kuke cewa dama kune lokacin da suka auri mazajen nasu ba masu arzikin bane yawanci se bayan aure Allah yake buda musu daga falalarsa,
Don haka kema karki fitar da ran daga rabon ubangijinki, arziki Allah ke badawa kuma kowa rabonsa baze kaice masa ba, idan baku samu na duniyaba kwa samu mafifici na lahira,
Kedai ki dage da sana arki cikin gida mai mutunci Ku rufawa juna asiri ki rike ibadarki ki zauna agidanki ki kula da iyalinki cikin mutunci kuyi rayuwa cikin tausayawa juna da mutunta juna.
[5/6, 9:15 AM] Zakiyya Publisher Haskenews: Aljannarki take karkashin mijinki. Yake yar uwa kiyiwa mijinki fahimta mai kyau,
kidena ganin cewa kanku daya dashi
kidena ganin mijinki be isa dake ba
Kidena yarda ana fada miki cewa duk abinda na namiji ya iya kema zaki iya
Karki yadda arinka zugaki cewa kar kiwa mijinki biyaiya
Karki raina mijinki
Kar ki saka kanki acikin a irin wadannan matan da basu san kimar mijinsuba
Karki yadda ki zama mai wulakanta mjinki arayuwarki
Domin namiji gatane agareki
Namijji jigone arayuwarki
Namiji garkuwa ne awajenki
Namiji rufin asirinki ne.
Dayawa ana yiwa wasu matan hudubar da sam bai daceba ana zugasu ana nuna musu rashin ganin girman namiji, irin wadannan matan ki nisan cesu ba mutanen kirki bane, zasu hallakaki, irin wadann matan basa anfani da abinda da addini yace, sunfi maida hankalinsu gabin yahudawa, kedai kawai kiyi abinda ya dace kirinka tuna makomarki awajen ubangiji, Allah yasa mudace.
[5/6, 9:15 AM] Zakiyya Publisher Haskenews: Sannan Acikin rayuwar aure yan uwana, akwai tarbiya ta yara, ma ana tarbiyantar dasu bisa tafarki mai kyau, a nuna musu hanya da zasu bi suyi rayuwa mai inganci.
KU KOYAWA YARANKU HALAYE UKU
1 yawan gaishe da na gaba dash
2 Nutsuwa da barin wasa ahanya
3 Futa cikin kyakyawar futa
KU HANA YARANKU HALAYENNAN
1 Yawan yawace yawace
2 Yawan abokai ko waye barkatai
3 Rashin kunya da fadace fadace
KU RINKA KWABAR BAKIN YARANKU
1 Idan suna sa baki a maganar manya
2 Idan suna kawo tsegumi da gulma
3 Idan suna zagi ko karyata many a
KUYI MUSU HORO MAI TSANANI
1 Idan suna wasa da sallah
2 Idan suka fara kwadayi da roko
3 Idan suka fara karya da lalaci
KU KARA JAWO YARANKU AJIGI
1 Idan suka balaga
2 Idan basu da lafiya
3 Idan kuna gida azaune
KU KWADAITAR DA YARANKU
1 Nacin karatu da rubutu
2 Dagewa wajen cimma buri
3 Lada da nasara idan anbi hanyar Allah
KU NUNAWA YARA MAHIMMANCIN
1 Riko da addinin musulunci
2 Zumunci da ziyarar dangi
3 Lafiya lokaci dama da kuma kuruciya
KU DENA WANAN AGABANSU
1 Bayyana tsiraici mu amalar aure
2 Wasan banza na kuruciya
3 Bayyana rashin jituwa atsakanin Ku
KUYAWAITA AGABAN YARANKU
1 Karatun Alkur ani da salloli
2 Aikata gaskiya da rikon amana
3 Wadatar zuci da godiyar Allah
SUKEJIN TSORONKU TA HANYAR
1 Tsawatar musu in sunzo da wargi
2 Rashin barinsu babu abinyi
3 Takaita nuna musu so kuru kuru
KU DAGE KU CIREWA YARANKU
1 Tsoron mutuwa
2 Tsoron talauci
3 Tsoron wanda baya tsoron Allah
KU GOYI BAYAN YAYANKU INHAR
1 Sune keda gaskiya
2 Ba sabo suka aikata ba
3 Suyi abu domin kare mutuncinku
KUKE TSORATAR DA YARANKU
1 illar hadama
2 Fitinar rigima
3 Hadarin takama da girman kai
KU RINKA SANAR DA YARANKU
1 Asali da tarihi
2 Mutuwa da kabari
3 Dadi da rashin Sa
KU BAWA YARANKU HORO NA
1 Takaita cin abinci
2 karancin bacci da zaman hira
3 Watsar da dogon buri da sharholiya
0 Response to "YADDA AKE ZAMAN AURE A Yau"
Post a Comment