-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

RAYUWAR BUDURCI KAFIN AURE

RAYUWAR BUDURCI KAFIN AURE

RAYUWAR BUDURCI KAFIN AURE. 

Roko da yan mata sukeyi, da kuma kyautatawa tsakanin saurayi da budurwa.

Akwai  wani Abu da yan mata sukeyi wanda be dace ace sunayi amatsayin su na mata masu mutunci ba, kada ya zamana cewa kin maida dabi arki yawan rokon saurayi kudi, za a iya samun matsala atsakaninku saboda yau da gobe se Allah, za a wayi gari wanan kimar taki da yake gani an wayi gari ya ragu ko babu ma, kuma ze iya dena yi miki idan kina yawan tambayar shi abu, Amma akwai kyautata tsakanin ki da saurayinki ba wai dole bane seya baki kudi, saboda soyaiya kesa saurayi ya kyautatawa budurwa, bawai tilasba, ki tsaya amatsayinki na wanan kyautatawar a tsakaninku.

Sanan ki rufawa kanki asiri ki rike darajarki ta ya mace karki rinka yin abinda mutuncinki ze zube agaban shi.

Kada ki rinka bin saurayi shakatawa ba burgewa bane saurayi ya dauke ki ki tafi wai gun yawo a haka komai na iya faruwa, saurayine bafa mijiba idan mijinke ne ko inama kuje, don Allah ki kiyaye ki kiyaye wanan mutuncin ki rufawa kanki asiri da iyayenki da zuri arku da zaku haifa domin wata rana kema uwace.

[5/17, 11:40 AM] Zakiyya Publisher Haskenews: Sanan kuma akwai kawaye masu bata tarbiya,  duk iya tarbiyar da iyaye suka tsaya suka yiwa yaransu to wasu kawayen idan ba ai sa a ba sesun bata, don haka ki kiyaye irin wadanan kawayen.

Duk wata kawar da ba zata dora ki akan turbar bautar  Allah da komawa gareshiba, to wanan wallahi wanan ba kawar Kirki bace, dukanin kawar da data rinka kwadaitar  dake akan biye biyen nanaye da sharholiya to tabbas se kinyi nadamar kasan cewa tare da ita aranar lahira"

Kawar da zata kusan tar dake ga mahaliccin ki Allah itace kawa amma duk wacca zatai kokarin nisan taki da mahalliccinki to wanan ba kawa bace abokiya gaban kice aranar lahira, domin se kunyi baran baran da ita a gaban Allah mabuwayi koda kuwa anan duniya aminan juna ne ku, don haka seki san irin wacca za kiyi kawance da ita  ki kiyaye ki lura da dabi unta ya take me take aikatawa me take da niyar yi ma ana dai ki tantan ce wajan zabar aminiya ko kuma kawa da zaki ma amala da ita

[5/17, 11:45 AM] Zakiyya Publisher Haskenews: Magance wasu matsaloli da ake yawaitar samun su a lokacin yin aure ko kafin ayi aure, ya kamata agyara.

Ku shiryawa rayuwar aurenku, mafi yawancin aure yana mutuwa ne saboda ma auratan ranar bikinsu kadai suka shiryawa amma bawai rayuwar auren ba, da lilin hakan yasa da yawa se kaga sabani yana ta shiga tsakaninsu, saboda ba suyi ilmin rayuwar auren ba labarin ta kawai sukeji shiyasa suke ta shaholiya suna  zubar da kima da darajar auren nasu tin aranar auren ko kafin zuwanta 

Duk wadan da suka shiryawa rayuwar aurensu to hakika zaka same su suna zaman lafiya me inganci Wanda ko wannen su yake alfahari da kowa mijin yana jin DaDin zama da matarshi matar ma haka.

Amma duk wanda zaka zaka ga  daga anyi  aurensu bada dadewa ba har suna fara tsinkayar sabani a zaman takewar aurensu, to hakika irin wadanan ne ranar auren kawai suka shiryawa ba wai zaman rayuwar auren ba gaba daya.

[5/17, 11:45 AM] Zakiyya Publisher Haskenews: Matsalar tana farawa ne tin daga zuwa zance, karya tayi yawa shi yai mata karya ita kuma son abin duniya shu kuma ya samu dama duk abinda yake so daga nan kuma se aita tafiya ahaka.

Daga shi har ita ba Wanda yake zama ya fahimci dan uwansa, kamata yai kusan kanku tin kafin Ku shiga sanan Ku fahimci kanku dakyau, amma da yawa ba a haka kawai auren akeyi,

Sanan kuma yayin da aka zo aure kafin ayi auren ana yin wasu abubu da base daceba yadda na fada abaya, kamar wasu bidi o i da akeyi, kamar free weeding da ake yi, bama free weeding din ne me ban haushiba abinda ake aikatawa a free weeding din, kamar  hotuna da akeyi kaga saurayi da budurwa suna cakumar juna suna rungumar juna suna aikata abubuwan da basu dace ba, dama a iya hoton za atsaya base an tabe  junaba, a gaskiyar magana wanan Abu da ake be dace ba, ai kunya cikon addini ce, ko ba komai akwai kunya, kuma Allah da Annabi basu ce mutun ya zamo Mara kunya ba,  kuma basu  yadda da mutum ya dinga nuna jikinsa ga   kowa ba, musamman ma mace, domin babu wani littafi, ko hadisi, ko a aya acikin surah, da yace haka, yanzu da hankalinki da hankalinka zaka rinka aikata abinda ka sani kai da kanka be dace ba 

Babu lefi idan anyi photoya, amma asan abinda ya kamata anayi kuma wani abun takaicin hoton ba a iya su ze tsaya ba, dukka se an bazasu ko ina mutane sun gani, ko wani kato da gardi da kare da doki ya gama ganema suffar mata, sekace baka da kishi, ya kamata ka zamo me kishin matarka shine kana soyaiya, sanan ga wani abu DJ da ake daukowa araba dare anayi maza da mata wasu kaga sun hade harda mata a cakude, ana rawa tabbas shedanu zasu zo suma sabida duk wani harkar kida da rawa na shedanci suna wajen gaka daga nan matsala ta samu an zubar da mutunci da albarkar auren tun  anan wajen ina lefin ace mata kawai ayi abun na hankali babu rashin kunya ba fitsara aci. 

Da wanan ma kawai ayi walima mana atara jama a, a mutunce aci asha, ba tare da anyi badala ba ko  shashanci da shirme duk wannan ba waye bane, kada Ku sake ku yadda kuyi  aure da aikata zunubai da abubuwan da basu dace ba amatsayin wai wayewa ko zama nanci, daga anan ake kwashe albarkar auren tin awaje idan anje aita samun matsala, Allah yasa mudace yabawa kowa nagari tsakanin maza da mata

[5/17, 12:14 PM] Zakiyya Publisher Haskenews: Sanan ki lura ki gane masoyinki na gaskiya Wanda sonki yake yi da gaske, da Wanda shi kuma kawai jikinki yake so idan biki hankali kin kulaba da ya samu abun da yake so shikenan kuma ze tafi ya barki, ki rage son abinda duniya da son abin hannun na miji duk lokacin daya fuskanci son abin hannun shi kikeyi ze iya amfani da wannan damar ya bata miki rayuwarki, amma ki sani kice kika jawo kuma kiyi kuka da kanki, duk lokacin da aka fada miki gaskiya karki tsiwa kar kiyi rashin kunya ko kiyi izgili zauna ko saurara abinda aka fada miki mai kyau kuma kiyi amfani dashi domin masoyinka ne me fada maka gaskiya, ki kula da tarbiyarki kanki Wanda iyayenki suka baki kema idan kin haifi naki yaran kiyi musu yarbiyar.

[5/17, 12:14 PM] Zakiyya Publisher Haskenews: A yayin da kike zaman gidan kafin aure, kada kice ke dole se irin wanda kike so ne zezo gurinki,  watakil shi kuma komai naki be masa ba, ko kadan ba laifi kika masa ba, ko wani dam Adam akwai abinda ya masa tareda dan mutum.

Misali ace shi yana son doguwa ke kuma baki da tsayi to wanan kadai ze iya hana ya soki, kome kike dashi inda baki da tsayi to shi ba zaki shiga zuciyar shiba, wani ma muryar kice matsalar da  zata sa bazaki kwanta masa  a zuciya ba wani kuma tsarin rayuwar kine be masa ba,kedai ki tsare  mutuncin kanki.

Kada kiyi gaggawa kada ki zamo daya daga cikin wasu mata mara sa lissafi da tunani, yawanci wasu mata suna aure ne da Wanda ya shirya yin aure ne bada wanda suke soba se daga baya suzo suyi dana Sani, aurefa ba abune wanda ake yinsa na kwana uku ko biyu ko sati ko kuma wata ko shekara, Aure abune da ake fata har iya tsayin rai da mutuwa har abadin abadan har karshen rayuwa har acikin aljannar ubangiji (s w t) ana fata akasance tare,

[5/17, 12:14 PM] Zakiyya Publisher Haskenews: Kar kiyi gaggawa karki gajiya   karkiyi sare yar uwa, kar ki yadda a zuga ki ace ki auri wani don kin rasa zabi ko don ba wani ko ace miki ai zaki fara sonshi a hankali, zaman aure fa ba wasa bane kuma ba karya bane.

Kibi ahankali insha Allah zaki nasara, Ita soyaiya tamkar lada ce da ita idan zaka hau seka saka kafafunka sanan ka tabbatar sun daidaita ta yadda babu wani maganar wullowa, sanan shi so  idan ka tashi hawansa seka bisa asannu idan ka bishi da gaggawa aikuwa zakaga gaggawa idan kuwa ka bishi sannu ahankali seya kaika birnin nasara da kyakyawan sakamako,

Abin nufi anan shine ita soyaiya a sannu ake binta kuma da hakuri juriya imani da tawakkali domin kuwa makamai ne na yaki da farin cikin yauda kullum, ki sani duk Wanda ya dogara da Allah to ze Isar masa, don haka ki nutsu  kada kiyi zabin tumun dare da kanki.

[5/17, 12:14 PM] Zakiyya Publisher Haskenews: Sanan kuma yar uwa kada kice zaki damu, dan baki samu mijiba, jinkirin aure baya sa mace ta rasa kima da mutunci, rashin kamun Kaine me saka arasa wadannan abubuwa masu daraja ga ya mace, bafa akanki aka fara rabuwa da saurayi ba kina tareda shi kullum cikin neman zabin Allah kike karki sake son na miji ya rufe miki ido duk na mijin da kika fahimci bashi da lokacin ki baya baki kulawa baya miki maganar aure kulluma se soyaiya idan an hau online ba text ba kira sedai chart kawai, to gaskiya ba kece ta asalin ba, duk namijin gaske masoyin kwarai baze bari se a chart Ku rinka magana ba,  duk sanda kike masa ki rinka Neman zabin Allah karki yadda ya wulakan taki tun kafin ya aure ki, wallahi idan kika bi  Allah kika rike addinin ki kika kiyaye munana kaba ira kika bi iyayenki to wallahi kin gama za kiga Allah yai miki zabin Alkhairi, babu Wanda yasan damuwar ka fiye da Allah babu wanda ze maka maganin ta seshi ka nemi temakon sa ta hanyar yawaita addu o i domin Allah. Baya watsar da bukatun Wanda ya kai kukan sa wajen sa.

0 Response to "RAYUWAR BUDURCI KAFIN AURE"

Post a Comment