Rayuwar budurci kafin aure
Rayuwar budurci kafin aure,.
yan mata arage kwadayi da dogon buri awajan zaben mijin auren.
Ku saurareni kuji wanan maganar.
Amatsayin ki na budurwa me hankali da nutsuwa, wacca kike da burin gobenki tai kyau,
Kada ki rinka bin saurayi yawan shakatawa, ba birgewa bane saurayi ya daukeki ki boshi wai yawon shakatawa, ahakan komai na iya faruwa saurayi ne bafa mijinki ba idan mijin kujema ko ina ba matsala, don Allah yan uwana Ku kiyaye ku kiyaye wanan mutuncin naku ku rufawa kanku asiri da iyayenku da zuri ar da zaku haifa domin watarana Ku iyayene.
Ku lura Ku gane masoyanku na gaskiya Wanda yake sonki da gaske da wanda shi kawai jikinki yake so idan bakiyi hankali ba daga ya samu abinda yake so shikenan kuma.
Ku rage son Abin duniya da abin hannun na miji duk lokacin daya fuskanci cewa abin hannunshi kikeso ze iya amfani da wanan ranar ya bata miki rayuwarki, amma kisani kece kika jawo kuma kiyi kuka da kanki.
Duk sanda aka fada miki gaskiya kar kiyi tsawa kar kiyi rashin kunya ko kiyi izgilanci, ki tsaya ki zauna ki saurara kiyi amfani dashi domin mai sonki shine me gaya miki gaskiya.
Ki kula da tarbiyar iyayenki Wanda suka baki kema idan kin haifi naki yaran kiyi musu tarbiya.
0 Response to "Rayuwar budurci kafin aure"
Post a Comment