Muhimmin Bayani Akan Tallafin N50,000.00 Da Shirin Rance Da Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayarwa Ga Kananan Yan Kasuwa
Muhimmin Bayani Akan Tallafin N50,000.00 Da Shirin Rance Da Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayarwa Ga Kananan Yan Kasuwa.
Shin Kana Daya Daga Cikin Wadanda Suka Cike Tallafin N50,000.00 Na Presidential Conditional Grant Scheme Da Kuma Shirin Rance Na Presidential Palliative Programmes Transforming Businesses, Improving Lives Da Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayarwa Kwanannan? Idan Amsar "Eh" Daure Ka Karanta Wannan Muhimmin Bayani.
A satin da yagabata ne dubban al'umma suka samu tallafin N50,000 na gwamnatin tarayya mai taken "Presidential conditional grant scheme (pcgs) wasu kuma na cigaba da jiran nasu tallafin, hakan yasa muka samu daruruwan sakonku dan gane da wannan jiran na za'a tura masu ko ba za'a tura masu. kar ku manta ku kasance da mujallar https://www.haskenews.com.ng/
Dafarko yana da kyau mu sani cewa shi wannan tallafin na gwamnatin tarayya ya kasu kashi biyu, kashi na farko shi ake kira grant wato tallafi. A wannan tsarin adadin tallafin dai ya kai N50,000.00 (naira dubu hamsin), kuma an tsara tallafin ne domin tallafawa masu kananan sana’o'o miliyan daya a kananan hukumomi 774 da muke da su. A halin yanzu an rufe cike aikace-aikacen tallafin na farko kuma kuma gibi na farko ne suka samu tallafin, gibi na biyu kuma na cigaba da jiran nasu tallafin. Ana tsammanin za'a fara turawa wadanda basu samuba kwanannan, wasu jahohi kuma na cigaba da tan-tance BIO data na wadanda zasuci gajiyar shirin. Yanar gizo da zaku shiga: https://grant.fedgrantandloan.gov.ng/
Tsarin tallafi/rance na biyu ana masa taken presidential palliative programmes transforming businesses, improving lives. A wannan tsarin yankasuwa manya, matsakaita da kanana ne zasuci gajiyar shirin, amma wannan tsarin bashi ne za'a bayar daga N500,000 zuwa N500,000,000 musamman ga yan kasuwa masu rijistar cac. Shi dai wannan tsarin yanada ruwa na 9% a duk shekara. Kuma har ayau ana ci gaba da cikewa ta yanar gizo kamar haka: https://loan.fedgrantandloan.gov.ng/
Tsare-tsaren tallafi/rance
Kashi na farko
- Sunan shirin: Presidential Conditional Grant Scheme (PCGS)
- Shafin tallafi : https://grant.fedgrantandloan.gov.ng/
- Adadin tallafi: N50,000.00
- Dole ne a samarda nin number kafin cikewa
Kashi na farko
- Sunan shirin: Presidential Palliative Programmes Transforming Businesses, Improving Lives
- Shafin tallafi: https://loan.fedgrantandloan.gov.ng/
- Adadin tallafi: N500,000.00 - N500,000,000.00
- Dole ne a samarda nin number kafin cikewa
I can't understand ,speak in english
ReplyDelete