YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI
YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI
Shi dai zama da talakan miji kamar yanda ya kamata duk matar aure da ta tsinci kanta da zama da irin wannan miji ta kasance mai tawakkali da fahimta sosai in dai tana so ita da mijinta su kasance cikin aminci da soyayya da kuma kaunar juna. Sannan kuma sai ta dauki wasu matakai guda biyar kamar haka:
1. Na farko dai sai ta zamanto mai tsantsar hakuri
2. Sannan ta zamo macce mai addini
3. Ta zamanto macce mai kyautatawa
4. Ta kasance macce mai sadaukarwa
5. Sannan na karshe ta kasance mai yawan tattaunawa da mijinta
1. Ta kasance mai tsantsar hakuri, wannan hakurin nata shi zai haifar mata da wasu abubuwa da yawa na alheri a gidan aurenta. Dole sai ta kasance mai hakuri akan kyalekyali na rayuwa saboda halin rashi na mijin bazai iya samar mata da wadannan abubuwan ba. Yakamata tun kafin aurensu ya kasance saboda Allah zata so shi ba wai don wani abu ba yin hakan shi zai samar mata da zaman lafiya tareda mijinta.
2. Ta zamanto macce mai addini wadda akoda yaushe tana kiyaye da yin sallah acikin lokacinta bata wasa, ta kasance duk wasu dokoki na zaman aure da addini ya kawosu tana kiyayewa dasu domin samun zaman lafiya a gidan aurenta.
3. Ta kasance macce mai kyautatawa, duk wata kyautatawa ta zaman aure da ya kamata macce ta yiwa mijinta ya kasance tana yi bakin iyawarta kamar misali ta fuskar ayyukan cikin gida daidai yanda macce zata iya yi. Misali a kauyuka akwai mata masu zuwa gona suyi noman abincin da za'a ci a gida, ko wata idan zatayi abinci sai taje rumbu ta debo hatsi ta surfa ta gyara sannan ta sarrafashi domin aci a gida, wata sai taje rafi ta debo ruwa, wata sai taje tayo itace na amfani domin ayi girki a gida to duk sai da hakuri da kuma kyautatawa wadannan ke faruwa domin hali na talauci ke kawo wadannan ayyukan, saboda ko a kauyen babban mutum mai kudi bazai bari matarshi tayi wadannan ayyukan na wahala ba sai a gidan talakan miji ake samun irin wadannan ayyukan.
4. Ta zamanto mai sadaukarwa, idan Allah Ya jarabci wanda macce take tare dashi da babu (waton wani talaka wanda ba matsiyaci ba) dole sai ta sadaukar da komai nata na rayuwa akan wannan mijin nata, komai da take dashi ta rika ji a ranta cewa ba nata bane na talakan mijinta ne, sannan kuma misali kamar idan tana wata yar sana'a ne shima yana daga cikin sadaukarwa tana taimakon mijinta da abunda take samu a sana’ar nan tata wajen maganace duk wasu lalurori na cikin gida hakan zai samar mata da zaman lafiya da kuma soyayya mai karfi tsakaninta da mijinta.
5. Abu na karshe shine mata ta kasance mai yawan tattaunawa da mijinta, kasancewarta tana yawan tattaunawa da mijinta tana bashi shawarwari bisa gaskiya kuma tana bashi karfina guiwa wurin duka damuwarshi ta rashi yana sanar da ita, ita Kuma tana nuna mashi tsananin kulawarta na halin da yake ciki kuma tana nuna talaucin da yake ciki baya damuwarta wannan shi zai taimaka masu wurin fahimtar juna da kuma zaman lafiya a rayuwarsu ta aure.
Ku kasance tare damu
0 Response to "YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI"
Post a Comment