Yadda ake zama da mazan zamani
Yadda ake zama da mazan zamani
Ki zamo mace ta gari, agidan mijinki. Gidan miji masarautace ga mace, shiyasa mace ta gari me sarrafa dukkan abinda ta mallaka na ilmi, hankali, wayewa da kwarewa rayuwa domin ganin ta zamar da masarautarta aljannar duniya, wajen kwanciyar hankali, more rayuwa, da cikakkakiyar nutsuwa ga uba da yayanta. Mace ta gari itace wacca tai fice da kwarewa, tare da yaukaka yaukaka soyaiyarta wajen inganta bangarori guda sha biyar, kamar haka, iya kwalliyar, girki, tarba, murmushi, magana, kallo rakiya, kwanciya, hira, tafiya, raha, rarrashi, da kwantar da hankali. Mace fa gari amatakin farko tana kusantar mijintane domin ta fahimci da bi u, da halayen sa, da bukatunsa, domin tasan yadda zata zauna da abinta. Mace ta gari babban burinta, cika siffofin da manzon Allah (s a w) ya siffanta mace tagari dasu. Mace ta gari tana zaman airene domin samun yardar Allah, azza wajallah, lazimtar addu o, i, da kyautata laduban tarbiya ta addinin musulunci agidanta da ya yayanta, tana kiyaye ibada da kamata tsoron Allah adukkan al amuranta. Mace ta gari tana fifita ilmi fiye da komai na rayuwarta, tana maida hankaki akan kyakyawar rayuwar ilmin acikin gidanta da yaranta, domin samun albarka da rabauta, har aranar gobe kiyama.
0 Response to "Yadda ake zama da mazan zamani"
Post a Comment