Shawara Kafin Aure
Shawara Kafin Aure
Mu Kyautata Rayuwarmu, ka zama mai kula ya kamata ka kiyaye rayuwarka, ka kula wanan,kada ka zamo mai hassada, kada kace kaima zakai hassada, ga Wanda yakema hassada, ka kyale mai hassada da sharrin sa, domin cutar dake zuciyar shi kadaima ta isheshi ba la i. Kada ka rama mugunta da mugunta domin wanan halin kaskanci ne, amma rama mugunta da Alkhairi wanan shine halin Annabawa, domin sune ababan koyinmu. Kyautata zato ga mutane koda sharrinsu ya bayyana gareka karara, kada ka kalli kanka amatsayin fiyaiye abainar jama domin Allah shine ma sanin asirai bayinsa, kuma shiriya a hanunsa take. Kaida ka shuryu ba wayenka ne ya shiryar da kaiba, ba kuma ilmin kaneba, ikon ubangijine kawai da kuma falalarsa agareka. Hakama rufin asiri da Allah yai maka, bawai yana nufin Allah yafi Sonka neba fiye da kowa, Sedai ya baka domin ya jarrabeka ya gwada halayyanka. Haka shima talauci, ko jinya, idan Allah ya dora maka, bawai yana nufin cewa Allah baya Sonka bane, a ah, sotaiyar tasa cema ta janyo haka, kuma ya zabe ka nema ya jarraba halayyarka.
Haka Kuma ka Kyautata Alkalaminka. Yana daga cikin ni imar da Allah yaiwa Dan Adam, na koyar dashi yadda zeyi bayanin Abinda yake ransa, ta hanyar furuci ko kuma rubutu, wanan ni imar kadai idan ka duba, zaka tabbatar da banbancin Dan Adam da sauran halittun Allah masu yawa, don haka wajibine agode masa kada a butulce masa. Kasani cewa ba a yimaka wanan ni i, mar bane, don kazo ka rinka tsinewa mutane da cakuda karya da gaskiya ta furucin ko rubutunka ba, domin ka sani duk abinda ga bobinka me sarrafawa ababan tambaya ne gareka, don haka ka kyautata furucinka da kalmominka, ta hanyar ambaton Alheri da tsayiwa akan gaskiya, da godewa Allah, da rokon shi tabbatuwa akan tafarki madaidaici.
Ka Tursasawa Zuciyarki Ka. Ita zuciyata tanada matukar bukatar saiti tayadda kada asake koda wasa abiye mata, domin kuwa duk Wanda ya biyewa son zuciyar sa, zata kaishi ta baro, domin dukkan gafala da nadama son zuciya ne tushensu, don haka dolene mu tursasawa zukatanmu kada mu biye mata abinda take so, mara kyau, kuma dole mu tursasawa zukatanmu don yin biyaya ga Allah, domin kuwa hakan shine ze jawo mana tsira a aduniya da lahira, ka fadawa zuciyarka ka gargadeta, ka kame hannunta ka kuma yi mata hisabi, ko ta samu tayi tanadi tin kafin lokaci ya kare. Duk mutum mai hankali rayuwar sa na karewa ne, yana kara kusantar ubangijin sa, ta hanyar bin umarnin sa, da nisantar akan abinda yai hani akan sa, ka tsaya kaiwa kanka hisabi, akan abinda ka aikata ko kuma kake aikatawa, akullum ka zamo mai nadama, mai imani, mai tunanin mutuwa, me zaka tarar meka aikata, mene makomarka, wanda yafi kowa daraja awajan Allah shine wanda yafi tsoron Allah, tareda kyawawan dabi u, ubangiji Allah yasa mu dace
Ya Zama na ka tabbar da wandanan abubuwa kafin kayi ayi aure. Kafin kayi aure, dole ka samu cikakken sani game da auren, ka idoji da sharadun da Allah ya gindaya acikinsa. Kafin kayi aure ya dace ka samu ilmin yadda zaka mu a malanci matarka, gurin mu a malar aure don gudun fadawa jagwalgwalo. Dole kasan cewa Kaine Wanda Allah ya dorawa alhakin ciyar da iyalinka, tifatar dasu, da neman musu lafiya, lokacin da suke cikin rashin lafiya. Ya zama dole ka samu cikakkiyar sana ar da zaka iya daukar duk wata dawainiyar iyalanka kafin kai aure, addini ma bai halatta Wanda baze iya daukar nauyin iyalansa ba yai aure. Idan kana son dorewar zaman aurenka, to seka samu kyakyawar niyya game da auren, ba don sha awa ba kawai, ko dan abokanka sunyi aure kaima kayi ba. Ya dace ka bayyanawa wacca zaka aura ainahin dabi unka, karka boyewa wadda zaka aura dabi arka, idan dabi arka Mara kyau ce to se kayi kokarin gayarawa. Kada ka nunawa wacca zaka aura kai mai wadata ne alhalin ba haka abin yake ba, ka nuna mata gaskiyar yadda kake, to Akwai wacca zata soka a yadda kake, bazaka rasa mosoyiya ba, abinda wani baya so, to tabbas shi wani yake so, ya dace ka fahimci dabi ar wacca zaka aura kafin Ka aureta, domin kasan yadda zaka zauna da ita. Idan kayi dogowar soyaiya kafin aure, idan kuka fahimci suna san junanku, kuma kun fahimci junan ku, sekuyi aurenku, domin doguwar soyaiya tafi kama da yaudara. Ka nunawa wacca zaka aura kana girmama iyayanka da kuma yan uwanka, kuma kaima ka girmama iyayenta da yan uwanta. Idan ka mallaki wadanan abubuwa to tabbas bakada haufi akan auren da zakayi, to zakayi shi cikin jin dadi da kwanciyar hankali.
0 Response to "Shawara Kafin Aure"
Post a Comment