Cikakken Bayanin Yadda Ake Zaman Budurci
Cikakken Bayanin Yadda Ake Zaman Budurci
YADDA AKE ZAMAN BUDURCI,
kafin kiyi aure, alokacin da kike gida, ya kamata ki kula sosai da rayuwarki da kanki duka, kisani cewa ke macece mai kima da mutunci, Allah yai miki ni ima, ni imar da Allah yayiwa musulma, baiwar da yayi mata babbace mai tsoka, ta yadda musulunci ya inganga mata hanyoyin cigaba, ya tsareta, yayi mata kariya, yai mata kariya ga mutuncinta, ya tabbatar mata da kimarta, ya kawar mata cuta da wulakanci, domin ta dawwama mai tsarkakarkiyar zuciya, mai tsarkin halitta mai tsararriyar jiki, kuma tsararriya daga abinda yake mai lalata rayuwa, abin tsarewa daga dalilai na Karkacewa, da juyawar dabi a, da zamewa. Duk irin wadannan kariya da ubangiji ya baki, da ni imar da yai miki amatsayinki na mace, se kema ki taya kanki tsare kanki, tareda kamewa da kula, da tanuni mai kyau, da tsoron Allah, tare da inganta rayuwarki, ta hanyoyi masu kyau, hanyoyin da ma aiki ya doramu akansu. Babu mafi darajar dabi a ga mace, musamman budurwa zata rike, kamar kame kanta, ta kame kanta daga mutanen banza,koyin mu a, mala da wadanda basu cancanta ki kulasu acikin rayuwarki ba, ki tuna cewa daga budurwa kirki ake zama uwa ta gari ga zuri arki, tin farko idan ke budurwar kirkice, to har zuwa gidan aurenki ke mutuniyar arzikice, ko zuriya kika fara tarawa, zaki san yadda zaki tafiyar dasu zaki musu ingantacciyar tarbiya, wadanda suma zasu zama abin alfahari, sanan ki zamo mai kunya aduk halin da kike, domin cewa duk macen data rasa kunya to akwai matsala sosai, saboda idan har babu kunya, babu abinda bazaki iya aikatawa, saboda kin cire wanan kunyar gareki.
Ki zamo mai bibiyar imaninki, cikar kyawun imaninki awanan duniyar, shine cikar kyawun fuskarki aranar lahira, ki sani cewa ita mace yar kwalisa, akullum takan bata lokacin tane ajikin mudubi domin ta bibiyi kyawun fuskarta, kuma ta tabbatar dashi ajikinta, amma ita mace mai addini kuwa, takan bibiyi imanintane, ta hanyar karatun alkur ani, da sauraran wa azozi daga bakin malamai, da kuma karanta littafan ilmi na addini, domin ta kara karfafa imanin nata, hakika wanan itace kyakyawar wayewa wacca babu nakasu acikinta. Sanan ki mutunta kanki, idan ya kasance kinada kyawu, kada ki sadaukar da kyawunki akafafan sada zumunta na zamani, don kawai kina bukatar wata yabawa, ko dangwalawa, ko don ace kinada kyau acikin mutanen duniya, matukar baikiji tsoron Allah kin kiyaye dokokinsa ba, to hakika babu Wanda ze kalleki sau biyu aranar alkiyama saboda tsananin munin da zakiyi, bayan kin karbi hukunci awajan ubangijinki, kamaninki zasu sassaba, saboda haka kada ki biyewa masu yada hotunansu akafofin sada zumunta ko makamantan haka. Kisani cewa Abu mafi tsada ga ya mace shine, kunya, Ubangiji ya fada mana acikin alkur ani, budurwa tazo tana tafiya acikin kuya, Allah be siffanta mana tsawonfa ko dirin halittarta ba, sai unbangiji ya siffanta ta da abu mafi tsada dake tare da ita wato kunya. Kunyar ya mace baya tauye mata komai cikin kamalarta, sedai ya kara mata kyau da tsada, ta yadda matsiyaci baze iya taya farashinta ba, don haka kiji tsoron Allah, kunya da kamewa sune siffofin tsadarki wajen mutanen kirki na kwarai, futar da tsiraici da maida kanki a arha, baze jawo miki kowa ba se kattin banza yan bata lokaci, don haka ki kiyaye wajan sanya sutura mai rufe jiki duka kada ki zamo mai tallan kanki a arha, ga zunubi da kike iba wajan ubangiji ga zubar da mutunci da kike, wanda baze jawo miki komaiba se dana sanin da bata da amfani, idan har baki daina ba.
Ki zamo mace ta gari aduk inda kike. Macen kwarai bata da lokacin hira mara ma ana da kawaye, mace ta gari lokacinta da nutsuwarta sukan wanzu sukan wanzu ne kadai alokacin da take nazari bisa abinda ya shafi addinin ta game da yadda zata gyara gobenta domin haduwa da mahaliccita lafiya, ki zama mace tagari, ki rike wadanan abubuwa, domin tabbatuwarki na mace tagari wacca tasan ya kamata. Aduk inda kika samu kanki ki zamo mai godiya ga Allah.
Ki zama mace mai kula da addiniki.
Ki zama mai amfani da ilminki, idan kina da ilmi mutukar bakya aiki dashi to babu amfanin wanan ilmin naki.
Karki zama mace mai wulakanci ko gadara da rashin mutumci ga jama a kidak ki zama Mao girmama jama da mutuntasu tareda karramasu da ganin girmansu.
Ki zama mai kunya, saboda kunya tana karawa mace kyau da ado sabida yan cikin addinin musulunci.
Nutsuwa da kamala agareki ya zama wajibine amatsayin ki na mace domin wanan siffarce daya dace da mace.
Ki zama mai hakuri hakuri ma yana da kyau saboda duk macen da bazata iya hakuri ba akwai matsala domin hakuri yana temakawa rayuwar dan adam.
Yin biyaiya ya zama wajibi muddin bai sabawa sha ri ah ba tun daga kan iyayenki har mijinki.
Ki zama mai tsafta da kwalliya don mace yar gayuce ako ina.
Ki zama kwararriya ta wajen girki da iya sarrafa abinci, duk iya karatunki indai baki iya abinci ba, to shima akwai matsala.
Haka kuma yake yar uwa alokacin da kike zaman budurci, ki zama me tsare kanki, domin rayuwar duniya yar kadan ce kuma ita lahira itace mafi Alkhairi ga masu tsoron Allah, kada dukiyar ki ko kyawunki ya rudeki, domin baze amfanar dake komaiba agaban ubanginki.
Ina miki gargadi da tsoratarwa tare da tunatarwa agareki,akan abinda Annabi ya fada s, a, w. cewa an bijiro mishi da wuta kuma yaga mafi yawan ma abota cikinta mata ne, kuma ina kara tunatar dake cewa Annabi s, a, w. ya kara cewa, kema kina daga cikin mata kuji tsoron fitina kuji tsoron mata domin farkon fitinar data samu bani isra ila ta kasance daga matane, kuma ki kare kanki daga wuta kisani ke gajiyaiyyace ke bazaki iya jure azabar wuta ba, domin ko dutse idan ya fada wuta narkewa yakeyi inake ina irin wadanan manyan duwatsun?, ki kare kanki daga wuta sanan kuma ki amsa kiran mai kira na gaskiya, kuma ki sani dukkan wanda yabar wani Abu domin girman Allah, Allah ze musaya masa mafi Alkhairin sa, kuma lallai lahira itace makoma mafi kyawu daga komai.
Karki zamo mai yawan buri na dukiya ko wasu agugu cikin duniya, me kike nema kike nufi na siyan kayan alatu masu tsada Mara adadi domin kawai kiyi amfani dasu, kina fidda daruruwan nerori da kudinki kina saya, ba ace karki siyaba amma akimanta domin almubazzaranci ma babu kyau, ki shiryawa lahirarki ba duniya ba, su wadanann kayan dakike siya masu tsada kina sawa, watarana, fa idan kika mutu zaki barsu anan duniyane, bazaki tafi dasuba illa idan kin mutu asaki a kabari cikin linkafani mafi arha, daga cikin suturar da ake sanyawa, su wadancen kayan masu tsada ba zasu amfaneki da komaiba.
Ki tunatar d ranki da ita cikin wanan makabartar shine wajan kwanciyarki, don haka ki kiyaye ki tsaya kiyi rayuwa mai kyau ingantacciya, domin samun rahamar ubangijinki.
Haka kuma yayin da kike zaman budurci agida, yana da muhimmanci ki zama wayayya mai aji, kisani cewa bawai girman kai da jijji da kai da izza da isa sune aji ga ya mace ba, a ah, ba haka bane
Abinda ake nufi da mace mai aji, duk wani abinda zatai ba zata bar alama da zata zamo barazana ga mutuncinta ba, kome zatayi cikin kulawa da nutsuwa da taka tsantsan take yinsa, wanda dole duk wanda yaga tsarin tafiyarta seta burgeshi kuma tashiga ranshi
Karki dauka wayayyu matan da maza suke cewa suna so sune masu sanya matsatsun kaya suna futar da tsiraicinsu abaiyane suna tikar rawa suna tikar rawa akafofin sadarwa, wallahi sam basu maza suke nufiba, kisani cewa idan wayewa kiki dauka wana, to sam su mazan kwarai harda na banza ma ba haka suka dauketa ba, hatta abokan sharholiyar matan banzan to mata na gari sukeda muradin aura ba yan iskaba, wayewarki gurin da namiji be wuce kasan cewarki me ilmi da kamun kai da tarbiyaba tareda nutsuwa, ba duk namiji bane mace mai irin wanan halin banzan take wayayya agurinshi ba, ki kula da irin rayuwar da kike gudanarwa arayuwarki, kisan me kikeyi kafin lokaci ya kure miki, kisani tabbas duk abinda kika aikata arayuwarki, wata rana wanan abun ze bujuro miki, wanda a wanan lokaci baki da ikon da zaki hana faruwar hakan ko mai kyau ko Mara kyau, tabbas wata rana ze dawo gareki, amma kiyi kokari kiyi mai kyau, kar kyau, ko asali, ko dukiya, su rudeki awajan yin abinda kike so, kisani dukkan wadanan abubuwa masu wucewa agareki, kiyi kokari ki inganta yau dinki, domin gobenki tai kyau.
0 Response to "Cikakken Bayanin Yadda Ake Zaman Budurci"
Post a Comment