YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI
YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI
, yadda zaki tarbiyar yarki mace, Tarbiyar musulci itace tarbiyar da a ka ginata akan tsarin Alqur ani da sunna, cikin manufofin addinin musulunci, da wanan ne zaki bi gurin tarbiyantar da 'ya mace, Tarbiyar ya mace ba bata inganta seda ingantanciyar tarbiyar da na miji, musulunci ya bada falala ga tarbiyar mata, domin sune iyayen al umma, kuma rabin alumna. Hanyoyin tarbiyar ya mace yana farawa ne tin daga zabin miji ko mata, mata da miji masu tarbiya sune zasu iya bada ingantattiyar tarbiya ta musulunci, Mata da miji sune taurarin yaya matukar suna kan turban addini, to yayansu ma zasu bi sahu, Tsare halal da haram tarda addu a suma suna da tasiri wajen tarbiyar musulunci. Tarbiyar ya mace alokacin yarinta. Yawan yin karatun alkur ani da sauraranshi, tin daga haihuwar ya mace, yin hakan ze haifar mata da son qur ani hadi da son karanta shi, Karan tarwa da ilmantarwa a aikace tareda kiyaye ka i doji wajen siyan sutura, Tsaida sallah da sauran ibada a aikace, tare da ita, kuma da nuni ga mahimmancinsu da falalarsu, Koyar da ita kyawawan halaye da kyawawan dabi u kamar gaskiya, rikon amana adalci da sauransu.A koya mata sanin kimar ya mace, ta salon magana sanya sutura, tafiya, zama, wasa. A koya mata sanin inda ya kamata ta shiga, da inda be kamata ta shigaba, da Wanda zata zauna dashi da Wanda bazata zauna dashi ba. Asanyawa ko wace makoncinta da ban. Tar biyar ya mace A lokacin data kai shekara 13- 15. Sanya sutura ta Shari da koyar da ita cewa addinin musulunci ya girmamata ta hanyoyi masu yawa, koyar da ita abubuwan da suka shafeta a matsayinta na budurwa, tareda nuna mata gakkokin da suka rataya akanta na addini, zamantakewa da haduran dazata iya fadawa, idan bata kiyayeba. Bata yanci tareda tattaunawa da ita akan abinda ya shafeta domin Samar da mafita. Bata kariya daga mugayen kauye, Koyar da ita tsarin rayuwar ya ace don haka dole amatsayinki na uwa ki tsaya ki kula da tarbiyar yarki sosai
0 Response to "YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI"
Post a Comment