NASIHOHI MASU AMFANI
NASIHOHI MASU AMFANI
*KADA KAYI RIGIMA DA MUTUM UKU*
Mahaifi
Malami
Shugaba .
*2 MUTUM UKU DA MUTANE BASA KAUNA*
1-Mai kudi marowaci
2-Talaka mai girman kai
3-Mai neman rigima bashi da karfi.
*3 HALIN MANYA UKU NE*
1- Yin afwa ga wanda ya zalunceka
2- KA bawa wanda ya hana ka
3- Sada zumunta ga wanda ya yanke maka.
*KA DARAJA MUTANE UKU A DUNIYA*
1. Dattijo.
2. Malami
3. Iyaye
*KA TAUSAYAWA MUTUM UKU*
1. Tsoho
2. mace.
3. Yaro karami
*KADA KA MANTA ABU UKU*
1. Mutunci
2. addini.
3. Mutuwa.
*KA TSAFTACE ABU UKU*
1. Jikinka
2. Tufafinka
3. Zuciyarka.
*KADA KA DENA NEMAN ABU UKU*
1. Ilimi
2. arziki.
3. Aljanna.
*ABU UKU SUNA KARA IMANI*
1- Tilawal Al-Qur'ani.
2- Kiyamul-laili.
3- Azkhar.
*ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU UKU:*
1- Hakkin Wani
2- Dabi'ar Annamimanci
3- Hassada
*ABUBUWA UKU SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:*
1- Istigfari.
2- Tausayawa waninka
3- Sadaka
*IDAN ALLAH YA BAKA ABU UKU TO KA GODEWA ALLAH:*
1- Lafiya
2- Wadata
3- Basira
*KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA UKU:*
1- Mai yawan fushi.
2- Maras sirri
3- Marar tsafta (Kazama)
*KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU UKU:*
1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana.
3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa
*ABUBUWA UKU KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:*
1- Yanke Zumunta.
2- Zagin Sahabbai.
3- Mutuwa da hakkin wani
*MUTANE UKU KADA KA SAURARI MAGANARSU:*
1- Makaryaci
2- Magulmaci
3- Malami mai kwadayi da son zuciya
*MUTUM UKU KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA* :
1- Munafiki
2- Mazinaci
3- Maras kunya
*ABUBUWA UKU BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:*
1- Sallah
2- Aure
3- Jana'iza
*ABUBUWA UKU RIKO DA SU YANA SAMAR DA RABO A LAHIRA:*
1- Kokarin ibada
2- Kula da Nafila
3- Amfani da Halal a Rayuwa
0 Response to "NASIHOHI MASU AMFANI"
Post a Comment