MU KYAUTATA RAYUWARMU
MU KYAUTATA RAYUWARMU
, kazama mai kula, Maza ku tausaya mata, Su mata masu raunine. Kar kai amfani da raunin su ka zalunci rayuwarsu, Allah baze barka ba. Su masu raunin imani ne, koda yaushe su masu bukatar kulawa ne, saboda kasancewar hankalin su Dana maza ya banbanta sosai. Kullum burin su su sami jagora wanda ze nuna musu hanyar Aljanna da gaskiya, saboda kasancewar su masu yawan kuskurene masu saurin shiga damuwa. A koda yaushe suna bukatar akula dasu da addinin su, saboda addininsu ze iya samun rauni, ta dalilin rashin mai kula da tarbiyarsu. Ka dena tunanin cewa ta fika ilmi ta fika sanin komai, zata iya tafi da rayuwarta ita kadai ,saboda ilmin addinin da take dashi ko ilmin zamani, duk ilmin da take dashi idan babu jagora zata iya fadawa wani halin da bazata iya futar da kantaba. Duk abinda na miji zeyi seya fara hangowa akwai mafuta ko babu, idan babu mafita to baze aikata ba. Amma ita mace seta fara aikatawa sanan kuma zata nemi mafuta, kaga kenan tana bukatar nagartaccen mahaifi, dan uwa, ko miji Wanda ze dinga daidaita tunaninta. Ita mace duk abinda ya burgeta zata iya mantawa da wanan ilmin nata tai abinda zatai dana sani daga baya. Hakanne Allah ya sanya maza su zama jagora acikin rayuwar su, saboda kasancewar su masu raunine. Adon haka, yana dakyau ga maza, su kula su kuma gane cewa sune agaba, kuma sune jagaba ga mata kuma mata ababan tausayawane da saurare yayin da suka kawo kukansu.
0 Response to "MU KYAUTATA RAYUWARMU"
Post a Comment