-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI

YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI

YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI

amatsayinki na matar aure, ya kamata ki kiyaye kafafuwanki daga ficefice yawace yawace yawace kada ki sake kije wani waje batare da saninshiba, ko idan kinje unguwa kice zaki biya wani waje, ki tabbatar da da yardarshi tukun zaki futa, idan ba haka ba duk sanda ya gan ki wataran mutuncinki ze zube a idanshi, kuma duk inda kikaje bada saninshi ba acikin tsiniwar mala iku kike harki dawo, kada ki bari wani ya shiga gidanshi ba tare da yardar shiba, kada ki rinka nuna gazawa akan buka tuwar daya zo miki da ita, domin shi mijinki ne akwai hakkinshi akanki, wajibi ki kula da mutuncinshi Dana yayanshi da yan uwanshi da kuma kulada dukiyarshi da duk wani Abu nashi badda Almubazzaranci, ki kasance me alkinyamai kayan abincinshi, kizamo me tattali, kada ki muzan tashi ko ki masa gori, domin yin gori ga miji babbar masiface ga mace, sanan kuma ki kasance mai tsafta akoda yaushe kada ki bari mijinki yaji kina wari ko bashi, jin haka ze haifar da  matsala agarki dashima ki kasance mai tsafta ta ko ina agidanki, jikinki, yayanki,  da duka gidan, da ban daki, akoda yaushe idan akazo gidan ki ko ba aji yana tashin kamshiba to aganshi fes tax, ko ina, kiyawaita Sa tirare agidanki domin itama kanta tsabta cikon addinice, idan zakiyi azumin nafil, kada kiyi sekin tambayi yardarshi sanan domin idan kikai baki gayamaiba yazama laifi agareki awajan Allah harseda izininahi.

Abangaren abinci, Ki kasance kin iya girki ta kowana fanni, kada abarki abaya na gargajiya kona zanani nau i nau i  kuma  kada yazama koda yaushe idan zakiwa mai gida girki Abu daya zakinamai,  ah a kina canzawa lokaci zuwa lokaci idan da halima kullum akwai kalar abincin dazakiyi mai, ki zama mai lura da duka abubuwan cikin gida, kina kula da rufe abinci kada kibari abude da kuma sauran aguguwa na cikin gida, saboda rashin kula da haka na jawo illa da matsala acikin gida harta kai ga iyalai sun illatu, kizamo mai kimantawa wajan duk wani Abu da zaki dafa kina aunawa kada ki rinka dafa Abu kai tsaya ba aunawa ko ki mantawa, hakan ze iya jawowa ana barin abinci yai yawa aci abarshi , kinga hakan yazama Almubazzaranci, kizamto mai tsari acikin gidan ki kada kina Abu kai tsaye ba lissafi ,domin duk Abu idan za ai da tsari yafi kyau.

Kada ki bari mijinki yana rigaki tashi daga bacci, kafin ya tashi ki tashi kiyi duk wani Abu daya dace kiyi, tsaftace kanki da cikin gida da kuma yara, idan yazo cin abinci kada kibarshi shi kadai yazamto kina wajan , kucima atare ko kina bashi abaki, kina mai hira mai dadi da kalamai masu sanyaya rai idan da idan zafi ake kikunna fanka idan babu kidau mafici kina mai fifita, hakan ze sashi yaji dadi sosai ya rinkaji aranshi bashi da matsala indai yana dake, sanan kuma idan yazo futa aiki ko gurin sana arshi kada ki barshi kawai ya tafi, ki taso ki biyoshi, ki rakoshi har tsakar gida ko gurin motane ko mashin ne ko akafane harzuwa daidai inda ze futa, kina mai addu a kala kala da kalamai masu dadi ki nuna damuwarki akan ze futa yabarki cewa zaki kewa, ki Nuna kulawa bayan ya futa,  ki zamo mai nuna kulawa ayayin da mijinki ya futa tare da nuna damuwarki akanki da addu o in nasara agarshi, kina kirashi akai akai, ya yake, yana lfy, ya aiki, da sauran tarairaya da   kauna akan shi, hakan ze kara bashi kwarin gwiwa aduk abinda yasa agaba. Haka idan ya dawo gida ki taho ki tarbeshi da murnarki tare da nuna farincikin da wowarshi gida ki karbi abinda yake hannun shi, tare da yimai sannu da zuwa, ba tafiya zakiyiba ki tsaya kiyimai abinda ya dace kin dafamai ruwan wanka idan wanka yakeso yafara idan kuma abinci se faraci kin ajjiye dama ,kafinan ki tanadi ruwan sanyinki ko lemo Wanda zaki fara bashi yasha yaji sanyi aranshi, kada ki barshi shikadai se kin tabbatar ki bashi duk wata kulawa data dace

0 Response to "YADDA AKE ZAMAN AURE A WANNAN ZAMANI"

Post a Comment