MU KYAUTATA RAYUWAMU
MU KYAUTATA RAYUWAMU.
RAYUWA. Kazama mai kula, kana iya aikata kurakurai da dayawa arayuwarka idan baka kula, kana iya dace, kana iya samun akasin haka, ka lura da irin Wanda zaka zauna dasu, idan ka aminta da mutum, zaka samu dayan biyu, koka samu amini na har abada ko kuma ka dauki darasi na har abada, kada kai bakin cikin abisa abinda ka rasa, domin da Alkhairi da Allah yabar makashi , saboda Allah baya raba mumini da Alkhairi, Kayi Mu amala da mutane Kamar karatun littafi, ka goge Abu Mara kyau, ka manta da mara mahimmaci, ka Dade wajan Abu mai kyau, kada ka bari rayiwarka ta zama budedden littafi, yadda Wanda besan muhimmacin karatuba ze yaga maka ita
KA ZAMA MAI KULA. Awani lo
kacin wadanda bama tsammanin sukan kaunacemu, yayin da wadanda mukeso sukan yi burus damu, wadanda ka damu dasu sesu lalubo uziri alokacin da kake tsananin bukatarsu, alokacin da wasu suke tsaya maka koda ka bukaci su kyaleka, ya kamata ka fahimci hanneyen dazaka rike da wadanda zaka gaisane kawai daga nan kace se anjima, ka kasance da wadanda kan damu dakai akowana lokaci da yanayi, bawai wadanda kan damu dakai idan yanayi yai musu.
0 Response to "MU KYAUTATA RAYUWAMU"
Post a Comment