Ba Boka ba Malam: Yadda Zaki Mallaki Mijinki a Saukake
Ba Boka ba Malam: Yadda Zaki Mallaki Mijinki a Saukake
Yadda zaki mallake miji a saukake, kirinka yi masa halin mata wato irinsu kisisina shagwaba don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa, ki zamanto mai iya kwalliya kici ado koda ya kasance baza kije ko inaba, kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki kona gida alokacin daya shigo kibarshi ya huta tukun ya samu nutsuwa, ki zamo mai kirki ladabi da biyaiya ga mahaifaiyar mijinki kamar yadda zakiso shima ya zamo mai biyaiya ga taki,ki dinga karfafa masa gwiwa aduk abinda ki kaga yana nema ya karaya hakan zesa ya zama gwarzo acikin maza, ki rinka fadawa mijinki sau da yawa kina sonshi sosai, kirinka yawan sada zumunci ga mutanen gidansu kamar ziyartasu kiransu awaya ki rinka bashi wani Dan karamin aiki haka agida idan yai seki godemai sosai, hakan zesa ya kara dagewa, ki rinka karfafa masa zuciya wajan aikin alheri, idan yana cikin damuwa ki bashi lokacin ki kiji meke damunsa, kirinka yimai godiya abisa kula da yake dake ya Samar miki da abinci da muhalli abune mai girma, ki tuna cewa mijinki yana da damuwa da farin ciki saboda haka kirinka tunawa dashi wajan yanke hukunci, idan miji ya nuna damuwa akan wani Abu kankani da kikai mai to seki bashi hakuri kuma ki dena, idan har zaki kula da yin wadannan abubu kiyisu da zuciya daya to insha Allah komai zeyi daidai ki mallaki mijinki cikin sauki
0 Response to "Ba Boka ba Malam: Yadda Zaki Mallaki Mijinki a Saukake"
Post a Comment