
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power
Matakin na zuwa ne bisa wasu abubuwan da aka gano game da shirin wanda ba daidai ba.
A cewar gwamnati, daukan matakin dakatarwar na zuwa ne bisa gano wasu kura-kurai da suke makale a shirin, kuma, tunin aka ƙaddamar da bincike kan yadda aka sarrafa kuɗaɗen da aka fitar tun lokacin fara aiwatar da shirin.
Ministar Kula da Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Fatara, Betta Edu, ita ce ta sanar da hakan yayin da take magana ta cikin wani shirin labaran talabijin din ‘TVC’ a ranar Asabar, ta yi iƙirarin cewa wasu da suke cin gajiyar shirin ba sa zuwa wuraren da aka turasu aiki, amma har yanzu su na tsamamanin a biyasu alawus-alawus na wata-wata.
Edu ta kara da cewa wasu da suke cikin shirin sun kammala cin moriya tun 2022 amma har yanzu suna cikin jerin waɗanda ake biya.
You May Also Like
- HUKUMAR KWASTAM TA ƘASA TA BAYAR DA SABON BAYANI KAN DAUKAR MA’AIKATA DA TAKE GUDANARWA
- Kungiyar Lafiya na neman Jami'in Shirye-shirye (Program Officer) da Jami'in Tabbatar da Bayanai (Data Verification Officer)
- Tallafin YDPAT na 2025: Yadda Zaku Cike Shiri Haɗin Gwiwa Tsakanin Ma'aikatar Ci Gaban Matasa ta Tarayya (FMYD) da Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPC)
- Kada Ka Bari Wannan Dama Ta Wuce Ka: Gwamnatin Sokoto Za Ta Dauki Matasa 3,000 Aiki a Ma'aikatun Gwamnati Daban-daban (MDAs) – Cika Fom Kafin Oktoba 6, 2025
“Dole ne mu waiwaya baya mu duba shirin N-Power kuma mun gano akwai kura-kurai don haka mun dakatar da shirin a yanzu har zuwa lokacin da za a kammala gudanar da cikakken bincike kan yadda aka sarrafa kuɗaɗen shirin N-Power.”
Ta ce, dole su gano mutum nawa ne suke cikin shirin a halin yanzu da kuma bashin da ke tattare da shi tare da gano mutum nawa ne bashin ya shafa, a cewarta gabaki ɗaya suna son sauya fasalin tsarin N-Power da ma faɗaɗa shi.
“Abubuwa da dama su na kan faruwa. Mun samu mutanen da ya dace su fita daga cikin shirin tun shekarar da ta gabata amma har yanzu suna kan iƙirarin cewa suna koyarwa."
“Wasu lokutan idan muka tuntuɓi makarantu ko wuraren da aka turasu aiki sai a tarar ba su zuwa ba su nan gaba ɗaya. Ba su aikin amma su na ta iƙirarin cewa suna bin bashin alawus na wata tawas ko wata tara. Kusan kaso 80 cikin 100 ba su aikin amma suna ta neman a biyasu albashi." Ina ji ta
0 Response to "DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power"
Post a Comment