Bashi: Sako Daga Ƙungiyar Manoma Shinkafa ta ƙasa wato RIFAN
Bashi: Sako Daga Ƙungiyar Manoma Shinkafa ta ƙasa wato RIFAN
Ƙungiyar Manoma Shinkafa ta ƙasa wato RIFAN ta umarci ya'yan ƙungiyar da suka karbi bashin kuɗin noman shinkafa na Anchor Borrowers dasu biya kuɗaɗen ko su bayarda shansherar shinkafa:
Ƙungiyar ta bada umarnin ne bayan da tayi wani zama da hukumar DSS a ranar 29/8/2023 akan zancen biyan kuɗin bashin na Anchor Borrowers.
Ƙungiyar ta manoman shinkafa tace ƴaƴan ƙungiyar zasu biya bashin kuɗin noman shinkafar ne na shekarun 2018, 2019, 2020 da kuma 2021.
Haka kuma ƙungiyar ta umarci ya'yan nata dasu biya kuɗaɗen a cikin asusun kungiyar kamar yadda hukumar ta ayyana a cikin takardar umarnin da ta fitar mai dauke kwanan watan 30/8/2023.
Haka kuma uwar kungiyar ta umarci shugabannin kungiyar na jahohi dasu haɗa kwamitin da zai karbo bashin ga ya'yanta da sukaki biyan kudin.
0 Response to "Bashi: Sako Daga Ƙungiyar Manoma Shinkafa ta ƙasa wato RIFAN"
Post a Comment