Tarihin Maryam Shetty
Tarihin Maryam Shetty
An haifi Maryam Shettima ce a jihar Kano, a shekarar 1979. Ta yi digirinta na farko a jami’ar Bayero da ke Kano, inda ta yi karatu a fannin lafiya, inda ta ƙware a fannin gashi.
Ta kuma samu digirinta na biyu a jami’ar Stratford da ke Birtaniya inda ta karanta fannin kula da ƙashi na ɓangaren wasanni. Maryam ta kasance a cikin likitocin tawagar Najeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a birnin Landon a shekara ta 2012. Baya ga wannan, Maryam ta yi kwasa-kwasai da dama a wasu cibiyoyi na ƙasashen duniya, ciki har da Amurka. Duk da cewa ba ta taɓa yin takara ba, ta kasance ƴar siyasa a a jam'iyyar APC mai mulki. Ta kasance a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Kuma shahararriya ce a shafukan sada zumunta na Najeriya.
Source: https://www.google.com/amp/s/www.bbc.com/hausa/articles/cd1gqrq5mr5o.amp
k.b.sodawa
ReplyDelete