Kalaman Kauna 2023/2024
Kalaman Kauna 2023/2024
Aminci Allah ya tabbata agareka mutum na gari, mutumin na farko da soyaiyar shi tai tasiri araina , ka shayar dani ruwan zumar soyaiya, kulawar da kake banice take karamin kaimi asoyaiyar ka,se nakeji nafi kowace mace Sa a da dacen nagartaccen masoyi kamar ka, idan na rufe idanuna kai nake gani haka ma idan na bude kai nake gani acikin tunani na ma Kaine gaba koda ina bacci ko ido bude hakika kayi tasiri matuka, acikin rayuwata, ka zamo fitalar rayuwata mai haskata idan ka futa daga rayuwata zata zamo duhu tamkar duhun dare, ka kan yimin gizo a idanuwana koda yaushe idanuwa na basa gajiya da ganinka hubbyna, ganinka ke daukemin dukkan damuwata murmushin ne ke ebemin kewata murmushi mafi kyauwun da yake bayyana hasken annurin fuskarka masoyina, inason naganka, ina matukar jinka araina dear, yaushe zaka zo? zanso naji ranar zuwanka domin na dandasa maka ado da kwalliya Wanda zasu saka farin ciki kasan banda buri irin na faran ta maka rai, burina naganka cikin walwala da nishadi bana son bacin ranka komai kankantar sa, ina jiranka abin kauna
0 Response to "Kalaman Kauna 2023/2024"
Post a Comment