Code da zaku saka domin toshewa ko dakile fitar kuɗi a bankinku
Code da zaku saka domin toshewa ko dakile fitar kuɗi a bankinku
Abu ɗaya da yakamata kasani cewa masu ƙwacen waya sunfi damuwa da sim card dinka fa, akwai wasu dake gefe wadanda da zarar an saci wayarka to su sim card din suke buqata SBD su kwashe maka dukiyarka dake bankinka, SBD ansan dai duk taqamarka shine ace kana da kudi a banki.
Kana ankarewa an sace maka waya to kada ka tsaya tunanin wani kiran bankinka ko zuwa banki cikin gaggawa, domin idan kiransu zakayi kafin su ɗaga kuyi magana tunin anyi maka abinda za'ayi.
Haka ma idan zuwa zakayi nan ma kafin kaje ka shiga cikin bankin anyi abinda za'ayi.
Hanya mafi sauqi shine ka ari wayar wani dake kusa dakai domin toshe bankinka ta yadda kuɗi ba zai fita ba sai dai ya shiga, ina nufin da kanka zaka iya kulle account dinka ta yadda kuɗi ba zai fita ba sai dai ya shiga.
Kusan kowanne banki akwai hanyoyin toshewar kada kuɗi ya fita, ga jerin bankunan da hanyar toshewar:
1.Access Bank: * 901 * 911 #
2. Zenith Bank: * 966 * 911 #
3. GTB Bank: * 737 * 51 * 74 #
4. WEMA Bank: * 945 * 911 #
5. First Bank: * 894 * 911 #
6. Key Stone Bank: * 7111 * 911 #
7. UBA Bank: * 919 * 911 #
8. FCMB Bank: * 329 * 911 #
9. Sterling Bank: * 822 * 911 #
10. Unity Bank: * 7799 * 911 #
11. Fidelity Bank: * 770 * 911 #
12. Heritage Bank: * 745 * 7 #
I3. Ecobank * 326 * 911 #
14. Union Bank * 826 * 911 #
15. Stanbic Bank * 909 * 911 #
16. Polaris Bank * 833 * 911 #
Zaka iyayi a kowanne layi ba lallai sai layinka ba, kawai bayan kasaka account number zasu buƙaci kasaka lambar da kakejin alert na wannan account din, shikenan zasu kulle kuɗi ba zai iya fita ba, duk randa kayi swap kuma to dole sai kaje bankinka sune zasu iya budewa komai yadawo yadda yake.
Allah ya tsaremu, a guji saka waya a aljihun gefe na riga ko aljihun gaban riga. Ka tabbatar wayarka tana inda ana kai hannu zakaji.
Daga Lecturer Aminu Muhammad Kaura
Dan Allah kuyi sharing Dan Wasu Su anfana
0 Response to "Code da zaku saka domin toshewa ko dakile fitar kuɗi a bankinku"
Post a Comment