Labari Mai Daɗi ga Waɗanda Suka Cike Aikin Kidaya na NPC[Enumerator da Supervisors]
Labari Mai Daɗi ga Waɗanda Suka Cike Aikin Kidaya na NPC[Enumerator da Supervisors]
Hukumar ƙidayar jama'a ta kasa ta sayo kayan aiki, zata raba ga ma'aikatan wucin gadi a faɗin ƙasar nan.Hukumar ta sayo motoci da babura da jiragen ruwa domin zirga-zirgar ma’aikata da kayan aiki a fadin kasar nan. An yi hakan ne tare da gyarawa da samar da kayan aiki ga dukkan ofisoshin jahohi 37 da na kananan hukumomi 774 don gudanar da ayyuka masu inganci domin gudanar da ƙidayar jama'a ta 2023.
Gudanar da ƙidayar dijital yana buƙatar samar da wutar lantarki akai-akai ba kawai a cikin birane ba har ma a cikin ƙauyuka kuma da wuya a isa yankunan ƙasar don cajin PDAs da sauran kayan aiki. Bisa la’akari da yadda wutar lantarki ke fama da ita a fadin kasar nan, hukumar ta sayo janaretoci da powar bank
da kuma sanya na’urar samar da wutar lantarki a fadin kasar nan.
Marubuci: Ahmed El-rufai Idris
0 Response to "Labari Mai Daɗi ga Waɗanda Suka Cike Aikin Kidaya na NPC[Enumerator da Supervisors]"
Post a Comment