Gwamnatin Jihar Kano ta Buɗe Shafin Cike Tallafin Karatu ga Hazikan Ɗalibai
Gwamnatin Jihar Kano ta Buɗe Shafin Cike Tallafin Karatu ga Hazikan Ɗalibai
Gwamnatin jihar Kano zata bayar da scholarship zuwa ƙasashen ƙetare na ɗalibai masu First Class.
Wannan yana daga alqawarurrukan da gwamnatin ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.
SHARUƊAN DA AKE BUKATA SUNE:
—Ya kasance mai nema cikakken ɗan jihar Kano ne
—Ya kasance ya gama digiri da First Class a jami'ar da take shaidar tantancewa a hukumance.
—Ya kasance mai ƙoshin lafiya
ABUBUWAN DA AKE BUƘATA SUN HADA DA:
—Shaidar zama ɗan jihar Kano
—Takardar haihuwa
—Shaidar gama makarantar firamare
—Shaidar kammala jarabawar sakandare (WASC/GCE/SSCE)
—Shaidar gama digiri mai ɗauke da First Class.
—Transcript da makamantansu
Za'a kai waɗannan takardu ne sakatariyar tantancewa dake tsohon dakin taro na ofishin sakataren Gwamnatin Kano kan titin Wudil Road.
A kula: KADA A WUCE SATI 2 BAA KAI WADANNAN TAKARDU BA.
Akwai website da mai nema zai shiga ya cike bayanan sa wato. http://www.kanostate.gov.ng/resumption-postgraduate-scholarship-kano-state-indigenes-first-class-honours-degree
A saurari ƙarin bayani na gaba.
Aminu Rabiu Tela
Mai wayar da kai (na sa kai) akan harkokin tallafin karatu na gwamnatin Kano.
0 Response to "Gwamnatin Jihar Kano ta Buɗe Shafin Cike Tallafin Karatu ga Hazikan Ɗalibai"
Post a Comment