Yadda zakayi registration na NDE domin samun tallafin N20,000 duk wata harna tsawon wata uku
Yadda zakayi registration na NDE domin samun tallafin N20,000 duk wata harna tsawon wata uku
Shidai wannan program mai suna Registration of unemployment person ana ma wa mutane register ne wanda basuda aikinyi kuma a kowanne gari anayin wannan registration ɗin a Federal secteria na wannan garin ofishin NDE National directorate of employment kodai wani office nasu da suka sanar wanda ko wanne jaha tanada nata
Amfanin wannan abun shine kaman ƙidayane na marassa aikinyi a ƙasa wanda hakan zai taimakawa Gwamnati tasan matakan da zata ɗauka akan rashin aikin yi da kuma sanin adadin mutanen da suke zaune basuda aikinyi a halin yanzu
Haka kuma zai taimaka sosai idan antashi rarraba aiyuka koh kuma wani tallafi toh ƙila ayi amfani da wannan ƙididdiga domin ganin suwa ya dace suci gajiyan wannan abun sosai fiyeda wasu, wasu mutane suna ganin wannan shiri nada alaƙa da shirinnan na SPW special public work wanda shekarun baya Gwamnati tayi zataba mutane 1000 aiki a kowanne LGA sannan a biyasu naira 20,000 duk wata harna tsawon wata uku wanda yanadaga cikin muraden Gwamnati na rage raɗaɗin talauci ga alumma amma kuma haryanzu bamu sami official sanarwa data nuna hakaɓa daga hukumar
Yadda zakayi registration na NDE Registration of Unemployment person shine
Kanemi offishin National directorate of employment na garinku wanda yawanci sun sanar kuma sunsa iya lokacin da za a samesu sai mutum ya tafi da National I'D card wato katin ɗan kasanka sauran bayanan duk zaka iya badasu koda ba bakine wanda suka haɗada
Suna
Lambar waya
Jinsi
Matsayin karatu
Shekaru
Dadai sauransu, sannan ba a wannan registration a online a dai yadda sukace saboda haka sai a kiyaye
Allah ya bada sa a
Please yaoushe zasu kulle registration
ReplyDelete