MATSALAR MATAN MU A YAU JINNIL ASHIQ
A YAU MAGANATA TA JUNNUN ASHIQ CE
MATSALAR MATAN MU A YAU JINNIL ASHIQ
MENENE JINNUL ASHIQ?
- JINNUL ASHIQ Wani irin aljani ne wanda yake
shiga Jikin Mata saboda tsananin soyayyar da
yake musu.
MENENE DALILAN SHIGARSA:
Ayawancin lokuta yakan shiga ne ta dalilin
SOYAYYA. amma awasu lokutan yakan shiga ta
wasu dalilan sannan daga baya ya juye ya zama
na soyayya din.
WACCE IRIN CUTARWA YAKE YI??
Daga cikin nau'in cutarwar da yake yiwa 'Yan-
Mata akwai:
1. Yakan Kore musu samari. komai soyayyar da
saurayi yake ma budurwa, sai ita kuma taji ta
tsaneshi. koda kuwa ita ce ta fara furta masa
soyayyar.
2. Yakan sanya ma budurwa Bakin-Jini mai
tsanani. ko kuma ya hana su samarin zuwa
wajenta. Ko da sun furta suna Qaunarta, amma
babu damar suzo wajenta zance.
3. Yakan rika zuwa yana saduwa da yarinya. zata
rika ganinsa yana zuwa mata amafarki yana
saduwa da ita. Acikin Siffar Saurayinta ko
mahaifinta, ko yayanta, ko kuma wani mutum
wanda ta sani ko kuma wanda ma bata sani ba.
4. Motsawar jinyoyi kala-kala da zarar anyi mata
maganar aure. sai kaga ta kama zlciwon kai da
zazzabi ba dare ba rana.
5. Daukewar Sha'awa. yarinya zata rinka ji acikin
ranta cewar ita fa bata son aure. kuma zataji
bata bukatar duk wani Namiji.
6. Wata ma idan abun ya fara nisa, ko unguwa
zata je, sai ta rika jin kamar wani yana tafiya
abayanta.. To Aljanin ne yake rakata.. Kuma yana
bibbiyar mazajen da suke kallonta awaje. da
zarar wani ya furta yana sonta, to Aljanin zai
shiga zuciyarsa ya sanya masa waswasi. har ya
shiriritar da shi.
7. Akwai wacce idan abun yayi nisa Aljanin zai
rika zuwa mata AFILI QARARA yana saduwa da
ita. koda da rana ne.
8. Akwai wacce aljanin zai rika sanya mata
saurin Fushi tana fada da samari. da zarar sun
fara soyayya da mutum sai taji Duk duniya bata
da Makiyi kamarsa.
9. Akwai wacce Aljaninta Har warning yake
yiwa samari. zai kira mutum ta waya. yace masa
Kar ya Qara ganinsa tare da wance.
0 Response to "MATSALAR MATAN MU A YAU JINNIL ASHIQ"
Post a Comment