Yanzu Yanzu: Anfara Cike Aikin Immigration
Yanzu Yanzu: Anfara Cike Aikin Immigration
Bayan sanarwar da Hukumar shige da fice ta ƙasa (Immigration) ta fitar a satin da yagabata na daukar sabin ma'aikata a yanzu haka shafin na daukar ma'aikatan ya fara aiki. Ku biyomu acikin wannan shafin namu mai albarka www.haskenews.com.ng domin kawo maku bayanai kan yadda zaku cike aikin kuma kuyi nasara.
Dafarko, yanada kyau mu sani cewa hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta bayyana cewa 5,000 ne za'a dauka a bangaren IMMIGRATION don haka yanada kyau idan zamu cike mu tabbatar mun bi ka'idodi da dokoki da hukumar ta gindiya.
Ku muyi gaggawa mu dare mukaranta abubuwanda da ke a kasa
Yadda zaka nemi aikin Immigration service
Da farko zaka shiga wannan link din https://cdcfib.career career domin cikewa
Ko ka latsa nan
Abubuwan da ake buƙata yayin cikewa
- 1. Dole ya kasance kaiɗan Nigeria ne
- 2. Kanada National I'D card
- 3. Yakasance kanada takardan makarantanka a hannu na abunda kakeso ka nema
- 4. Dole ya kasance kanada certificate daga asibiti na medical fitness kuma asibitin ya kasance na Gwamnati
- 5. Dole ya kasance kanada ɗabiu mai kyau kuma ba a taba kamaka da wani babban laifi bah
- 6. Dole ka haye gwajin kwayoyi wato dai sai anma gwaji saboda a tabbatarda baka shaye shaye
- 7. Ba aso yazama kanada nakasu a wurin al amrar kuɗi
- 8. Ya kasance ɗan shekara 18 zuwa 30 koh kuma 35 ga likitoci da masu magun guna (doctors and pharmacist) kuma kada tsawo yayi kasada 1.65m ga maza 1.60m kuma ga mata
- 9. Faɗin ƙirji kada yayi kasa da 0.87 ga maza
- 10. Sannan anaso. Yakasance kanada illimin computer kaɗan wannan ba dole bane inkanadashi zaka samu wani amfanin da wanda basudashi barasu samubah
- 11. Ka tabbatarda cewa duk wani certificate da kake dashi ka gabatardashi alokacin da ake dubah takardunka domin baza a karɓa bah idan har angama
Matakan aiki da akedasu (position)
- Category A: SUPERINTENDENT CADRE
I. SI conpass shine wanda suke da kwarewa akan fannin lafia wato doctors kuma sun gama NYSC ɗinsu wanda suka karanci MBBS kenan
II. DSI conpass: shikuma wannan wanda suka karinci sanin magun guna wato pharmacist kuma suka gama NYSC ɗinsu
III. ASI conpass o8 shikuma shine wanda duk wani mai degree koh HND wasu fanni daban kaman computer science, physics, history da sauransu zasu cika
- Category B INSPECTOR CADRE
Sukuma wanna sune na masu NCE da kuma diploma koh Advance NABTEB
- Category C ASSISTANT CADRE
I. Immigration Assistant iii compass shikuma idan kanada GCE koh NECO da sauransu wato wanda suka gama secondary school kuma sukeda credit guda huɗu 4 kada ya wuce zama biyu
II. Immigration Assistant iii conpass o3 shikuma wannan shine na masu trade certificate a driving koh mechanic kuma suma ya kasance sun gama secondary school wato SSCE
0 Response to "Yanzu Yanzu: Anfara Cike Aikin Immigration"
Post a Comment