Domin samun sauki kan canjin Sabbin kudade Banki CBN ya fito da Shirin CASHSWAP
Domin samun sauki kan canjin Sabbin kudade Banki CBN ya fito da Shirin CASHSWAP
A yau ne babban bankin Najeriya CBN ya kaddamar da shirin Cashswap wanda zai taimaka wajen gaggauta yaduwar sabbin kudin kasar da aka sauya wa fasali, gabanin karewar wa’adin mako guda da ya saura.
An dai samar da wannan shirin ne musamman don mazauna karkara da kuma dai-daikun al’umma da ke da ka’idar abin da za su iya cirewa a duk rana.
A cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar, za a yi amfani da shirin wajen kara wayar da kan al’umma game da karewar wa’adin daina amfani da tsofaffin kudin Naira dari biyu da dari biyar da kuma dubu daya.
A cewar bankin, shirin zai bai wa ejan-ejan da ke da lasisi sauya wa kowane mutum guda kudin da ba su wuce Naira dubu 10 ba, kuma ba tare da biyan kudin kamasho ba.
Kafin samar da wannan shirin dai, tuni Majaliisar Dattawar Kasar da wasu gwamnoni suka bukaci karin wa’adin daina amfani da tsofaffin kudin da aka sauya wa fasali.
A hukumance dai, a ranar Talatar makon gobe ne za a daina amfani da tsoffin takardun kasar da aka sauya wa fasali.
0 Response to "Domin samun sauki kan canjin Sabbin kudade Banki CBN ya fito da Shirin CASHSWAP"
Post a Comment