Ma'aikatar Ilmi ta JIHAR BORNO ta Buɗe Shafin Daukar Malamai ga Masu Kwalin NCE, HND, B.Sc. B.A. B.Ed, B.Sc.Ed, PGDE da dai sauransu
Ma'aikatar Ilimi ta JAHAR BORNO ta Buɗe Shafin Daukar Malamai ga Masu Kwalin NCE, HND, B.Sc. B.A. B.Ed, B.Sc.Ed, PGDE da dai sauransu
Gwamnatin Jihar Borno, ta bude shafin intanet da za a yi amfani da shi don neman gurbin aiki sabbin malaman makaranta 3,000 da za ta dauka.
Sanarwar da ta fito ta hannun Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Ali Musa, ta bukaci masu sha’awar aikin kuma suka cancanta, da su je su shigar da bayanansu ta wannan adireshin na intanet: moeapplication.bornostate.gov.ng
Daga cikin sharuddan cancantar neman aikin kamar yadda sanarwar ta nuna, ban da wadanda suka haura shekara 50 da haihuwa.
Sanarwar ta ce za a rufe shafin neman aikin ne ya zuwa 31 ga Disamba, 2022.
Gwamnatin Borno, karkashin Gwamna Babagana Zulum, ta dauki matakin daukar sabbin malaman ne domin inganta fannin ilimin jihar.
ABUBUWAN AIKI - Masu nema dole ne:
- A. Kasance ya kammala karatun digiri na wata babbar jami'a
- B. Kada ya wuce shekara 50
- C. Ya mallaki aƙalla, ɗaya (1) NCE, HND, B.Sc. B.A. B.Ed, B.Sc.Ed, PGDE da dai sauransu
- D. Ya mallaki Certificate NYSC (Discharge or Exemption)
- E. Yasance ya shirya inda za'a iya tura shi kowane yanki na Jiha.
YADDA AKE NEMAN
I. Duk masu sha'awar cike aikin karantarwa zasu cika ta wannan hanyar haɗin yanar gizon: moeapplication.bornostate.gov.ng
II. Aikace-aikacen Portal, ranar Litinin 5th na Disamba, 2022 zuwa Asabar 31 Disamba, 2022.
ALLAH yasa mudace baki daya
0 Response to "Ma'aikatar Ilmi ta JIHAR BORNO ta Buɗe Shafin Daukar Malamai ga Masu Kwalin NCE, HND, B.Sc. B.A. B.Ed, B.Sc.Ed, PGDE da dai sauransu"
Post a Comment