-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Blockchain Scholarship Programme: Summary na abubuwan da aka tattauna jiya a LIVE Youtube session cikin harshen Hausa

Blockchain Scholarship Programme: Summary na abubuwan da aka tattauna jiya a LIVE Youtube session cikin harshen Hausa

Blockchain Scholarship Programme: Summary na abubuwan da aka tattauna jiya a LIVE Youtube session cikin harshen Hausa

1. Domineum Academy ta taya kowa da kowa murnar samun shiga Blockchain Scholarship Programme din da Gwamnatin tarraya ta tanadar.

2. Sun kara da cewa dik wanda yayi applying toh tabbas ya samu shiga, sai dai in bai yi applying ba. Dan tun asali, sun so ne su zabi mutam dubu 30 amma sun yi mamakin ganin yadda akayi tururuwa wajen applying. Hakan ya faranta masu rai sosai, shiyasa suka ba kowa chance, basuyi omitting dik wanda yayi applying ba. Gabadaya mutanen da ke cikin tsarin a yanzu haka 93,040 ne, kusan dubu dari kenan, amma still suna kan maganar su ta mutum 30k da suke so. Saboda haka, sun bada shawara cewa kowa ya mai da hankali a wannan sati biyun farkon da za a fara karatu, dan bayan sati biyun ne za ayi tankade. Bayan sati biyun ne za su zabi mutum 30k da suka fi kokari sai a shiga next phase dasu. So sun ba da shawara sosai a wannan fannin, sun umarci kowa da kowa da ya maida hankali ya dage sosai dan ganin ya samu abun da ya zo nema.

3. So kamar yadda muka sani dai, karatun sati 12 za ayi...Satin biyun farko (Pre Course) wadda Domineum Academy za su gabatar. Sati 5 na gaba (Main Course) Za ayi shi ne a portal na BSV Academy. Sati 5 na karshe kuma (Project) karkashin Domineum Academy tare da hadin guiwan Partners na BSV Ecosystem.

4. Sun ce a sati biyun farko, ba dole bane amfani da Computer amma in kana da shi zai taimake ka sosai, amma in mutum ya tsallake zuwa phase na gaba to gaskiya ya zama wajibi ya nemi system ko kuma zai rika samun tangarda a tafiyar. Duka abubuwan da za ayi a first two weeks, mutum zai iya amfani da wayar sa. Kawai dai abun da akeso shine, ka ba wannan Programme din lokaci dan yin karatu yadda ya kamata kuma in sha Allah za ka tsallake.

5. Akwai weekly meetups din da za a dinga yi ko wani weekend amma sai an shiga next phase kafin a fara, kuma za a hada kowa da mentor na Jihar shi, za su kuma sanar da inda za a dinga haduwa a ko wani satin. Halartar haduwar ba dole bane in ba ka da hali. Amma in har kana kusa kuma ba ka da wani uzuri to ina mai ba ka shawara da ka dinga halartan meeting din dan akwai mihimmanci sosai. Kuma if possible a rika zuwa da System, dan za ayi kusan hour 3-4 a wurin meeting din.


Allah Ubangiji ya sa mu fara a sa'a. Ya kuma bamu sa'a gabadaya. (ameen)


Daga : TV-5KURA

Engr zaharaddeen

0 Response to "Blockchain Scholarship Programme: Summary na abubuwan da aka tattauna jiya a LIVE Youtube session cikin harshen Hausa"

Post a Comment