YADDA ZAKI HADA WAINAR HANTA
YADDA ZAKI HADA WAINAR HANTA
Abubuwan bukata sune kamar haka;
1. Hanta
2. Magi Gishiri
3. Curry
4. Albasa da tumatir
5. Kwai
6. Man
7. Kayan Miya
8. Man gyada
Yadda zaki hada;
Da farko xaki tafasa hanta da gishiri da albasa. Bayan ya dahu, sai ki daka da turmi ya daku. Idan ya daku sai ki kwashe ki ajiye gefe. Daga nan sai ki dauko markadaden Mayan miyarki ki dibi kamar cokali biyu na miyan ki xuba akan hadin hantanki, sai ki dauko maggi da gishiri da curry ki zuba aciki, sai ki tafasa kwai ki yanka albasa da dan attarugu sai ki hada ki juya sosai. Daga nan sai ki dora man ki a wuta ki fara xuba wannan kullin akan tiran kamar yadda ake soya wainar fulawa, ki barshi ya gasu. Idan kin gama sai ki kwashe. Shikenan wainar ki ta yi, sai anyi serving!
Zaki iya hadata da wani sauce Idan kinaso kuma zaki iya ci hakanan.
0 Response to "YADDA ZAKI HADA WAINAR HANTA"
Post a Comment