Yadda Zaki Hada Springles a Gida
Yadda Zaki Hada Springles a Gida
Abubuwan Bukata;
1. Albasa mai Dan yawa
2. Vinegar
3. Maggi da gishiri
4. Man Gyada
Yadda zaki hada;
Da farko zaki sami albasarki ki gyara ta ki cire mata duk wata datti, sai ki markadata da blender, Idan ta markadu sai ki tace ki cire dussan ki bar ruwan albasar a bowl. Daga nan sai ki dauko vinegar kadan da maggi da gishiri, saiki fere dankalinkin ki wanketa, sai ki dauko peeler ki dinga peeling dinshi lefe lefe, saga nan zaki ga yana lankwashewa. Bayan kinyi wannan saiki dauko dankalinki ki tsoma shi a cikin ruwan albasar da kika tanada ki barshi yayi kamar minti ashirin zuwa talatin acikin ruwan. Bayan kin barshi na tsawon lokacin nan, sai ki daura manki maidan yawa a wuta amma ki saka ci a low heat, sai kisoya. Shikenan springle dinki yayi!
0 Response to "Yadda Zaki Hada Springles a Gida"
Post a Comment