Yadda Zaki Hada Chips Salad
Yadda Zaki Hada Chips Salad
Abubuwan bukata;
1. Dankali ( na Hausa ko Irish)
2. Heinz beans
3. Salad Cream
4. Kwai
5. Man gyada
6. Attarugu da Albarsa
7. Gishir da Maggi
8. Nama
Da farko zaki dauko dankalinki ki fere ki yankashi atsaye, sai ki barbada gishiri akai ki soya acikin mai. Idan ya soyu sai ki kwashe, kiyi strainining man data jikinshi. Sai ki dauko namanki ki yanka kanana ki saka albasa, kayan kamshi da gishiri da maggi sai ki daura a wuta ki dafashi, idan yayi laushi sai ki dan soyashi acikin mai ya Dan soyu, daga nan sai ki dafa kwanki ki yankashi atsaye shima. Bayan kinyi wannan sai ki dauko plate mai fadi ki zuba dankalinki akai, sai ki dauko sauran kayan gaba daya ki sakasu akan dankalinki, amma jerasu zakiyi yadda zaiyi kyaun gani, sai dauko salad cream dinki daga karshe ki zuba akai. Shikenan sai ayi serving!
0 Response to "Yadda Zaki Hada Chips Salad"
Post a Comment