Ma'aikatar Ilimi Ta Tarayya Ta Buɗe Shafin Cike Tallafin Karatu Na Bangarorin Ilimin Yarjejeniyar Wato "BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 2023/2024" Zuwa Ƙasashen Russia, Morocco, Hungary, Egypt, Venezuela China, Serbia, Romania
Ma'aikatar Ilimi Ta Tarayya Ta Buɗe Shafin Cike Tallafin Karatu Na Bangarorin Ilimin Yarjejeniya Wato "BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 2023/2024" Zuwa Ƙasashen Russia, Morocco, Hungary, Egypt, Venezuela China, Serbia, Romania
Bangarorin Ilimi Yarjejeniya "BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 2023/2024" tallafi ne ga ɗalibai masu neman gurbin karatun digiri na daya 1 wato undergraduate ko digiri na biyu wato Masters da kuma digiri na uku wato Ph.D a ƙasashe kamar su Russia, Morocco, Hungary, Egypt, Venezuela China, Serbia, Romania kyauta.
Bangarorin Ilimi Yarjejeniya "BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 2023/2024" ya kasu kashi biyu (2)
- 1. Bangaren Digiri Na Daya "UNDERGRADUATE STUDY"
- 2. Bangaren Digiri Na Biyu ko Uku "POSTGRADUATE STUDY"
1. Bangaren Digiri Na Daya "UNDERGRADUATE STUDY" acikin wannan tsarin ɗalibai da sukayi nasara zasu samu damar karatu a kasashe kamar haka: Russia, Morocco, Hungary, Egypt and Venezuela
2. Bangaren Digiri Na Biyu ko Uku "POSTGRADUATE STUDY" acikin wannan tsarin ɗalibai da sukayi nasara zasu samu damar karatu a kasashe kamar haka: China, Hungary, Serbia, Romania.
Sharuɗɗan Cancanta
Masu nema dole ne su cika ka'idodi masu zuwa:
- Duk masu neman digiri na daya dole ne su mallaki mafi ƙarancin cancantar kyakkyawan sakamako Bakwai (7) na (As & Bs) a cikin Takaddun Sakandare na Senior, WASSCE/WAEC (Mayu/Yuni) a cikin darussan da suka dace da fannonin karatunda suka haɗa da Ingilishi da Lissafi. Kuma takardun su kasance acikin jarabawar shekarar daya (1) ko biyu (2) na 2020 da 2021) ga ƙasashen da ba na Afirka ba kuma ga ƙasashen Afirka shekarun satifiket shine shekara ɗaya (2021) kawai. Matsakaicin shekarun dan takara su kasance tsakanin 17 zuwa 20.
- Masu neman digiri na biyu dole ne su riƙe digiri na farko tare da 1st First Class ko aƙalla 2nd Class Upper Division. Duk masu nema dole ne su kammala shirin NYSC kuma iyakar shekarun shine shekaru 35 don Masters da shekaru 40 don PhD.
Yadda Zaku Cike
Yadda Zaku Cike Tallafin Bangarorin Ilimin Yarjejeniyar Wato "BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 2023/2024" masu shawar cike wannan tallafin zasu ziyarci shafin ma'aikatar ilimi ta Najeriya kamar haka
Shafin Ma'aikatar Ilimi Ta Tarayya: https://fsbn.com.ng/scholarships
Shafin Cikewa Kai Tsaye: https://fsbn.com.ng/applicants/auth/register/45480
Shafin Karin Bayani: https://fsbn.com.ng/scholarships
0 Response to "Ma'aikatar Ilimi Ta Tarayya Ta Buɗe Shafin Cike Tallafin Karatu Na Bangarorin Ilimin Yarjejeniyar Wato "BILATERAL EDUCATION AGREEMENT (BEA) 2023/2024" Zuwa Ƙasashen Russia, Morocco, Hungary, Egypt, Venezuela China, Serbia, Romania"
Post a Comment