Yadda Zaki Hada yoghurt, fura mai ayaba da lemon danyar shinkafa da dankali a saukake
Yadda Zaki Hada yoghurt, fura mai ayaba da lemon danyar shinkafa da dankali a saukake
A yau na zo muku da wani sanfari na yadda zaki hada kayan sha a saukake acikin gidan ki batareda kin bada kudi an siyo maki a waje ba. Waddan nan nau'ukan kayanshi sunada matukar amfani a wajen Dan Adam shiyasa akeson kowace mace ta san yadda zata iya sarrafa su. Ku biyoni domin ganin abunda nake tafe dasu a yau.
Abubuwan da zan kawo muku sune kamar haka;
1. Yoghurt
2. Fura mai Ayaba
3. Kunun danyar shinkafa da dankali
1. Yoghurt
Abubuwan bukata;
Madarar gari
Nono sabon tatsa
Ruwa
Yadda zaki hada yoghurt dinki;
Dafarko zaki samu tukunyarki mai kyau kizuba ruwa kidora kan wuta ki bari tukunyarki ta tafasa saiki barshi ya huce kadan. Idan ruwan sun huce saiki douko madara kirinqa barbadawa kina damawa harya danyi kauri, kada ki bari yayi gudaji wato lumps. Saiki dauko nonon shanu mai kauri sabon tatsa, marar tsami sai kirinqa zubawa kina motsawa. idan kingama saiki rufe ki ajiye wuri mai dan dumi kibarshi na tsawon awa uku zuwa hudu haka. Bayan awannin da na ambata sai ki bude madarar zakiga tayi kauri sosai saiki zuba suga da flavour ma'ana kamshi ki motsa ya motsu saiki zuzzuba acikin robar da kika ta nada kisa a fridge yayi sanyi. Shikenan yoghurt dinki yayi, idan yayi sanyi sai ayi serving.
2. Fura mai Ayaba
Abubuwan bukata;
Fura
Yoghurt
Madarar ruwa
Ayaba
Yadda zaki hada;
Da farko zaki samu furarki mai kyau ki zubata a blender,ki zuba yoghurt, da madarar ruwanki, sai ki yayyanka ayabar ki aciki ki rufe. Daga nan sai ki markadesu suyi laushi sosai, ba'a so ki saka ruwa acikin markadenki, zaki ga yayi kauri sosai. Idan kina so zaki iya sa dan ruwa, ko ki kara madarar ruwan ki yanda zai saki, kuma idan kina bukata zaki iya sa suga, sai ki sa a Fridge idan tayi sanyi sai ayi serving.
3. Lemon danyar shinkafa da dankali
Abubuwan bukata;
Danyar shinkafa
Dankali
Dabino
Madara
Sugar
Citta
Kaninfari
Falavor
Yadda za ki hada;
Dafarko ana so ki samo Danyar shinkafarki wato shinkafar masa ko tuwo sai ki jika ta tare da dabinonki wanda kika riga kika bare. Bayan kinyi wannan sai ki dauko gyararren dankalinki ki yayanka ta yadda zai yi mi ki saukin markađe. Sai ki hada shi a cikin Danyar shinkafarki tare da dabinonki, ki sanya cittarki tare da Kaninfarinki, sai ki hada ki markada. Bayan kin markada kayanki, sai ki tace, sannan sai ki kawo suganki ki zuba daidai yadda kike bukatarsa. Idan kikayi wannan sai ki kawo Falavor ki zuba. Bayan kin gama hada lemonki kin ji komai ya yi miki daidai, sai ki sanya shi a cikin fridge domin yayi. Shikenan lemon ki ya hadu,sai ayi serving.
0 Response to "Yadda Zaki Hada yoghurt, fura mai ayaba da lemon danyar shinkafa da dankali a saukake"
Post a Comment