Yadda Zaki Hada Miyar Kabeji da Nama
Girki Adon Ya Mace: Yadda Zaki Hada Miyar Kabeji da Nama
Assalamu Alaikum, a yau zan kawo muku wani nau'in miya Wanda ba kowa yasan dashi ba. Wannan miyar da kuke gani ta kunshi abubuwa sosai a tattare da ita, domin kuwa tana dauke da sinadaran karin lafiya a jikin dan Adam. Wannan miyar ba kowace miya bace face miyar Kabeji wacce ake hadawa da nama.
Wannan miyar akan hada ta da farar shinkafa, taliya, dafaffiyar doya da kuma sauransu. Zaki iya kuma cin abunki hakanan batare da wani abun ba.Yana da kyau a matsyinki na 'ya mace ki koyi salo iri iri na sarrafa abinci akoda yaushe.
Abubuwan Bukata;
- Kabeji
- Nama
- Man gyada
- Attarugu
- Albasa
- Tumatir
- Magi
- Kori
- Tafarnuwa
Yadda zaki hada;
Da farko dai zaki samu kabeji ki yayyanka ta manya-manya sannan ki wanke ta da ruwan gishiri domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki sannan ki yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu zuwa uku ki jajjaga tareda attarugu da tafarnuwa.
Daga nan sai ki wanke nama, zaki iya amfani da kowane kalan nama kike bukata, sannan ki tafasashi tare da albasa da gishiri kadan. Bayan ta yi laushi, sai kiyayyanka kanana sannan ki soya sama-sama. Bayan haka, said ki dora tukunya a wuta, ki zuba man gyada kadan sannan ki zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa ki soya. Sannan ki dauko naman ki zuba ba tare da romon ba. Daganan sai ki zuba magi da kori ki gauraya su, sai ki jira su tafasa sau daya sannan ki zuba kabejin ki gauraya sai ki dan rufe. Bayan mintuna uku zuwa biyar, sai ki sake budewa ki gauraya sannan ki kara rufewa na tsawon mintuna uku sannan ki sauke.
Shikenan miyar ki ta dahu sai ki yi serving. A ci dadi lafiya!
0 Response to "Yadda Zaki Hada Miyar Kabeji da Nama"
Post a Comment